News
SUDAN: Likitoci sun yi gargaɗi game da ƙaruwar cutar ƙyanda a Sudan
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
An samu ƙarin ɓarkewar cutar ƙyanda a Khartoum, babban birnin Sudan, saboda faɗan da ake ci gaba da gwabzawa, ya hana aikin allurar riga-kafi, wani likitan yara ya faɗa wa manema labarai.
Da yake jawabi ta cikin wani shiri kan rayuwa a Sudan mai taken Sudan Lifeline, Dr Mohamed al-Taher, wanda ke zaune a Khartoum, ya ce ana fama da ƙarancin alluran riga-kafi, abin da ka iya janyo ɓarkewar cutuka a tsakanin ƙananan yara.
JAMB Tace za ta gurfanar da matashiya a kotu kan shirga karya a sakamakon jarrabawa
“Alhakin ma’aikatar lafiya ne ta samar da riga-kafi, amma ba za ta iya sauke wannan nauyin ba musamman ta fannin alluran riga-kafi,” in ji shi..
“Akwai ƙarancin alluran riga-kafin ƙyanda kuma tuni aka samu yaran da suka kamu da cutar, sannan ana tsammanin lamarin zai yi tsanani… Cutar na iya tsananta saboda jikinsu ba zai iya bijirewa ƙwayoyin cutar ba.”
Yayin da ake ci gaba da luguden bama-bamai a unguwannin birnin masu cunkoson jama’a, akwai matuƙar hatsari a yi ƙoƙarin kai wa ga asibitocin da ke can.
bbc ta rawaito cewa Ƙungiyar likitocin ba da agaji ta Medecins Sans Frontieres ta yi gargaɗin cewa yayin da mutane ke tserewa gidajensu, akwai ƙaruwar cutukan ƙyanda da rashin abinci mai gina jiki a sansanonin da ke cikin jihar White Nile, kudu da babban birnin Sudan.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
