Connect with us

News

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya gana da shugaban sojojin hayar Rasha na Wagner

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya gana da shugaban sojojin hayar Rasha na Wagner, Yevgeny Prigozhin bayan gazawar kungiyar a watan da ya gabata, in ji fadar Kremlin.

Advertisement

Kakakin fadar Kremlin Dmitry Peskov ya kara da cewa Prigozhin wanda ke jagorantar kungiyar sojojin haya na Wagner na daga cikin mutane 35 da aka gayyata zuwa taron da aka yi a birnin Moscow.

Ba za mu sake yarda da juyin mulki a Yammacin Afirka ba – Tinubu

Ya ce shugaba Putin ya yi bayani kan yadda yaƙin Ukrane ke gudana da kuma boren sojojin haya.

Advertisement

Tawayen da suka kaddamar a ranar 23 ga watan Yuni ya ɗauki tsawon sa’o’i 24.

A karkashin yarjejeniyar, an yi watsi da tuhumar Prigozhin kuma an yi masa tayin koma wa Belarus.

Advertisement

An yi ta ce-ce-ku-ce tsakanin jama’a tsakanin Wagner da ma’aikatar tsaron Rasha game da gudanar da yakin. Prigozhin dai ya sha zargin ma’aikatar da gazawa.

Sai dai a ranar Litinin, Mista Peskov ya ce shugaban Wagner na cikin kwamandojin da aka gayyata zuwa Kremlin kwanaki biyar bayan rugujewar rikicin.

Advertisement

Kamfanin dillancin labaran Interfax ya ambato Mista Peskov yana cewa “Shugaban ya yi bayani akan abubuwan da kamfanin yayi a fagen daga.

A cewar kakakin, ya ce Prigozhin ya shaida wa Mista Putin cewa Wagner ta goyi bayansa ba tare da wani sharaɗi ba. Ba a dai san inda shugaban na Wagner yake ba.

Advertisement

A ranar Alhamis ɗin da ta gabata, shugaban Belarus Alexander Lukashenko – wanda ya kulla yarjejeniya ta kawo karshen tashin hankali – ya ce Prigozhin yana ƙasar Rasha.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending