News
Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar sun yarda su yi sulhu da ECOWAS
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.
Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar sun ce a shirye suke su tattauna da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS).
Sabon Firaiministan Nijar Ali Mahamane Lamine Zeine ne ya bayyana ga manema labarai haka bayan tawagar Malaman Nijeriya ta ziyarci jagoran masu juyin mulkin Janar Abdourahmane Tchiani ranar Asabar a Yamai.
Gwamnatin Kano Ta Hukunta Wani babban sakatare Kan Zargin Badaƙala
Wannan ne karon farko da sojojin suka nuna alamar yin sulhu tun bayan da suka kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum ranar 26 ga watan Yuli.
A lokacin da ‘yan jarida suka tambayi Firaiministan kasar kan ko sojojin sun shirya yin sulhu, ya ce: “Eh, tabbas. Wannan shi ne abin da jagoranmu ya gaya wa (Malaman), bai ce ba zai yi sulhu ba.”
Firaiministan yana fatan nan da ‘yan kwanaki kadan masu zuwa za su soma tattaunawa da ECOWAS.
