Politics
Buba Galadima bayyana dakatarwar da aka yi wa Kwankwaso a matsayin Wasan Barkwanci na Nollywood da Hollywood”.
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Daya daga cikin wadanda suka kafa jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, Buba Galadima ya bayyana dakatarwar da aka yi wa shugaban jam’iyyar na kasa, Rabi’u Kwankwaso a matsayin “Barkwanci na Nollywood da Hollywood”.
DAILY POST ta rawaito cewa a ranar Talata ne wani bangare na jam’iyyar ta dakatar da Kwankwaso, tare da wasu mambobinsa bisa zargin “ayyukan kyamar jam’iyyar a tarurruka daban-daban”.
Majalissar Dokokin Jihar Kano Na Duba Yiwuwar Gyara Dokar Ilimi Ta 1963
Amma Galadima, wanda ya yi magana a wani shiri a gidan Talabijin na Channels a daren ranar Talata, ya ce tun da farko an kori shugabannin kungiyar da ta sanar da dakatar da Kwankwaso daga jam’iyyar NNPP.
Galadima ya kuma dage cewa jam’iyyar tana nan daram kuma ba ta da wani rikici kamar yadda ake yi.
Ya ce, “Lokacin da na ga hakan a kafafen sada zumunta, sai na dauka kamar wasa ne na Nollywood ko Hollywood.
wadanda aka kora su ne Boniface Okechukwu Aniebonam da Gabriel Agbor Major.