Connect with us

News

Kungiyar Kwadago Ta Kauracewa Zama Da Gwamnatin Tarayya Kan Yajin Aiki

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Shugabannin ƙungiyar kwadago ta ƙasa (NLC) sun ƙaurace wa halartar taron da Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Simon Lalong, ya shirya a Abuja.

Ministan ya kira zaman ne da nufin shawo kansu su janye yajin aikin gargaɗi da suka shirya shiga a yau dinnan nan.

Advertisement

Har Yanzu Majalisar Dokokin Gombe Ba Ta Tantance Kwamishinoni Ba.

Rahotanni sun ce shugabannin ƙungiyar ‘yan kasuwa (TUC) ne ƙaɗai suka halarci taron karkashin shugaba, Festus Osifo.

Ganawar da aka shirya farawa da misalin ƙarfe 3:00 na yammacin jiya Litinin, hakan ba ta samu ba sai ƙarfe 5:32 na yammaci sannan suka shiga taron.

Advertisement

Rahotanni sun ce an hana kowa shiga taron, amma Ministan kwadagon ya roƙi ‘yan jarida su yi musu uzuri yayin da su ke kokarin shawo kan batutuwa masu muhimmanci.

A ranar Juma’ar da ta gabata, NLC ta ayyana cewa ma’aikata a fadin kasar nan za su fara yajin aikin gargadi na kwanaki biyu daga ranar Talata 5 ga watan Satumba saboda halin kuncin da ‘yan Najeriya ke ciki.

Advertisement

Sai dai abinda ba a tabbatar ba shine, ko yajin aikin zai fara a yau Talata ko a’a

Yayin da yake hira da yan jarida ɗazu a Abuja, Ministan kwadago, Lalong ya ce bai samu zama da ƙungiyoyin kwadago ba kafin yau saboda har yanzu bai samu bayani daga ɓagarorin da abin ya shafa ba.

Advertisement

Ministan ya kuma yi kira da ƙungiyon NLC da TUC su dakatar da mambobinsu da sauran ƙawayensu daga shiga wannan yajin aikin.

Har Yanzu Majalisar Dokokin Gombe Ba Ta Tantance Kwamishinoni Ba.

Advertisement

Wani labarin kuma Hukumomi a jihar Kano da ke arewacin Najeriya sun kaddamar da rabon tallafin kayan abinci da na noma ga al’ummar jihar don rage musu raɗaɗin cire tallafin man fetur.

Gwamnatin ta ce ta fara raba shinkafa mai nauyin kilogiram goma-goma da masara ga magidanda, musamman waɗanda suke zaune a karkara.

Advertisement

Abu biyu aka ƙaddamar a yau Litinin, na farko rabon kayan noma da injinan sana’o’in hannu, sai kuma kuma rabon tallafin kayan abinci.

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ce sun yi tanadi mai yawa na kayan abincin da suka sayo daga gwamnatin tarayya don tallafa wa mutane musamman mata.

Advertisement

Gwamnan ya kara da cewa daga yau sun ƙaddamar da bayar da tallafin shinkafa buhu 297,000, inda za a ci gaba da raba wa masu ƙaramin ƙarfi a mazaɓu 484 na jihar da ke ƙananan hukumomi 44.

Baya ga wannan kuma, an raba wa mata da maza kayan noma ciki har da taki da injinan ban ruwa da na niƙan masara.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending