News
Akwai Yiwuwar Samun Mamakon Ruwan Sama Kamar Da Bakin Kwarya Nan Da Kwanaki 3 Masu Zuwa-NIMET
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Hukumar hasashen yanayi ta Najeriya Nimet, tace akwai yuyuwar samun mamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya a jihohi 25 na kasar nan, nan da kwanaki 3 masu zuwa.
Hukumar tayi hasashen samun ruwan sama mai karfin gaske a wasu yankuna na jihohin Sokoto, Kebbi, Kaduna, Katsina, Kano, Jigawa, Yobe, Borno, Gombe, Bauchi, Adamawa, Taraba, Benue, Niger, Kogi, Ondo, Edo, Delta, Bayelsa, Rivers, Imo, Akwa Ibom, Abia, Ebonyi and Cross River State.
Kotun sauraren kararrakin zabe Ta Sauke Wani Sanata Daga Kujerarsa
Kazalika hukumar hasashen yanayi ta kasa tace akwai yuyuwar samun ruwan sama kamar da bakin kwarya a jihohin Legas,Ogun da kuma Adamawa.
Hukumar tayi hasashen samun ambaliya sakamakon mamakon ruwan saman a ranakun Alhamis da lahadi.
Kazalika, an shawarci jama’a da kada suyi tuku yayinda dake ruwan.Kazalika, an shawarci jama’a da kada suyi tuku yayinda dake ruwan. Hukumar ta shawarci jama’a da su sanya ido don samun karin bayanai.
Kungiyar kwadago ta Kasa NLC ta sanar da kawo karshen yajin aikin gargadi na kwanaki biyu.
Wani labarin kuma Rashin wutar lantarki da ake fama dashi tun kafin yanzu ya kara tsananta jiya a nan Jihar Kano, A yayin da kanfanin rarraba hasken wutar lantarki na KEDCO ya tsayar da aiyukansa kacokan, Lamarin da ya haifar da daukewar lantarki baki daya a cikin birnin Kano.
Wata sanarwa da shugaban sashin sadarwar kanfanin, Sani Bala Sani ya fitar, Ya alakanta daukewar wutar lantarkin da yin biyayya ga umarnin kungiyar kwadago ta kasa na tafiya yajin aikin gargadi na tsawon kwanaki biyu.
Sanarwar da aka wallafa a shafin X na kanfanin, Ta baiyana cewar za’a cigaba da fuskantar matsalar daukewar wutar lantarkin, kasancewar yajin aikin gargadin zai ci gaba da kasancewa a yau Laraba.
Shima mataimakin shugaban kungiyar kwadago ta kasa reshen jihar Kano, Kwamared Ado Riruwai, ya tabbatar da cewar kungiyarsu ta rufe dukkanin wasu ofisoshin gwamnati dake jihar Kano, domin tabbatar da yajin aikin gargadin.
