Connect with us

News

Amarya Ta Kone Gidan Mijinta A Jihar  Adamawa

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Wata sabuwar amarya mai shekara 20 ta shiga hannu kan cinna wa gidan mijinta wuta a Jihar Adamawa.

Advertisement

An ruwaito cewar amaryar ta yi wannan aika-aika ne saboda rashin son angon nata.

INEC za ta tattara lauyoyin da za su yi shari’ar masu laifi 197 nq zabukan da suka gabata 

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa ita wannan amarya ta sanar da iyayenta cewa ba ta son yin auren kwanaki kadan kafin a daura.

Advertisement

Sai dai iyayen nata suka ce ba gudu ba ja da baya saboda sun riga sun raba katin gayyatar auren.

Bayan an daura auren ne ta sa wani mai tsubbu ya mata aiki ya sa mijin ya tsane ta har ta kai ga sakin ta.

Advertisement

Amma sai ta kasance maimakon mijin ya tsane ta, sai ita amarya ta bige da kara tsanar mijin nata.

Wasu rahotanni sun ce ita wanna amarya da mijin nata sun kulla wata yarjejeniya kafin daura aurensu.

Advertisement

Kakakin ’yan sandan Jihar Adamawa, SP Suleiman Yahaya Nguroje, ya ce ruwaito ita amarya tana cewa “Mun shirya [da mijin nawa] cewa zai sake ni bayan auren.

“Bayana mun sadu da shi na roke shi ya sake ni, amma ya ki,” a cewarta.

Advertisement

Amaryar, wadda a halin yanzu take hannun ’yan sanda ta amsa laifin da ake tuhumar ta da aikatawa, kuma kwamishinan ’yan sandan jihar Adamawa, Afolabi Babatola, ya sanar cewa rundunarsa na kan bincikar lamarin.

A wani labarin kuma INEC za ta tattara lauyoyin da za su yi shari’ar masu laifi 197 nq zabukan da suka gabata 

Advertisement

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

Advertisement

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending