News
Wasu Ƴan Bindiga Sun Jikkata Ƴan Sanda Biyu Tare Da Sace Mutum 7 a Abuja
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Ƴan sanda biyu sun samu raunuka sanadiyyar harbi da bindiga, yayin da aka yi garkuwa da ƴan gida ɗaya mutum bayan da wasu ƴan bindiga suka tsananta kai hare-hare a yankin karamar hukumar Bwari da ke babban birnin tarayya Abuja.
Ƴan bindigar sun harbe wani mutum mai matsakaicin shekaru, mai suna Alhaji, wanda ya jagoranci ƴan sanda wajen daƙile garkuwa da mutum bakwan ƴan gida ɗaya.
A ƴan kwanakin nan, ƴan bindiga sun mamaye ƙauyukan da ke ƙarkashin ƙaramar hukumar Bwari, suna yin garkuwa da mutane tare da kashe su.
Wani mazaunin Bwari, Isaiah Samuel, ya ce lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Larabar nan, lokacin da ƴan bindigar suka kai farmaki garin Zuma 1 da ke unguwar Bwari.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ƴan sandan babban birnin tarayya Abuja, SP Adeh Josephine, a martanin da ta aike mata a sakon da ta aike wa wayar ta ta ce, “Zan dawo wurinki don Allah”.
A wani labarin kuma ‘Yan bindiga Sun Halaka Wasu ‘Yan Kasuwa 8 A Jihar Katsina
Babban Bankin Najeriya CBN ya sauya matsayarsa kan hada-hada da kuɗin intanet ko kuma cryptocurrency a ƙasar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma’a da ke umartar bankunan kasuwanci na Najeriya cewa su yi watsi da haramcin da ya saka kan amfani da kuɗin na crypto tu a 2021.
CBN ya ce yadda ake yayin kuɗin na crypto yanzu a faɗin duniya ya nuna irin buƙatar da ake da ita ta saka dokoki a kan sa.
“A watan Fabarairun 2021 CBN ya haramta wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi amfani da cryptocurrency saboda almundahanar kuɗi da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci,” in ji sanarwar.
“Sai dai kuma, abin da ke faruwa a duniya ya nuna cewa akwai buƙatar a kula da dukiyoyin hada-hada ta intanet wato Virtual Assets Service Providers (V/ASPs).”
Ya ƙara da cewa hukumar kula da hada-hada da hannayen jari za ta fitar dokoki da sharuɗɗan amfani da dukiyoyoin intanet ɗin.
Amma babban bankin ya jaddada haramcin yin kasuwanci, ko kuma mallakar asusun crypto ga bankunan kasuwancin su da kansu
