Connect with us

News

Tinubu Ya Amince Da Kamfanonin Jiragen Sama 3 Domin Jigilar Maniyyatan Aikin Hajjin Bana 

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Advertisement

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya amince da kamfanonin jiragen sama 3 domin jigilar maniyyatan aikin hajjin bana.

Hakan na kunshe ne ta cikin wata Sanarwa da Mataimakiyar daraktan hulda da jama’a na hakumar jin dadin alhazai ta kasa NAHCON Fatima Sanda-Usara ta fitar jiya a Abuja.

Advertisement

Tinubu Ya Amince Da Kamfanonin Jiragen Sama 3 Domin Jigilar Maniyyatan Aikin Hajjin Bana 

Kamfanin dillacin labarai na kasa NAN ya  cewa kamfanonin sun hada Air Peace Ltd., FlyNas da Max Air.

Haka zalika  amincewar da kamfanonin da gwamnatin tarayya tayi wani yunkuri ne na tabbatar da nasarar aikin hajjin ga maniyyatan na shakarar bana.

Advertisement

Kamfanin Air Peace zai yi jigilar miniyyatan daga jihohin Akwa Ibom, Anambra, Bayelsa, Cross River, Delta, Ebonyi, Edo, Ekiti, Enugu, Imo, Kwara, Ondo, Rivers da Birnin tarayya Abuja.

Sanarwar tace kamfanin FlyNas zai dauki mahajjata daga jihohin Borno, Lagos, Osun, Ogun, Niger, Sokoto, Kebbi, Yobe da jihar Zamfara.

Advertisement

Kazalika kamfanin Max Air zai yi jigilar maniyyata yan jihohin Bauchi, Benue, Kano, Katsina, Kogi, Nasarawa, Adamawa, Oyo, Taraba, Kaduna, Armed Forces, Gombe, jihar Filato da kuma  jihar Jigawa.

A wani labarin kuma Wasu Ƴan Bindiga Sun Jikkata Ƴan Sanda Biyu Tare Da Sace Mutum 7 a Abuja

Advertisement

Babban Bankin Najeriya CBN ya sauya matsayarsa kan hada-hada da kuɗin intanet ko kuma cryptocurrency a ƙasar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma’a da ke umartar bankunan kasuwanci na Najeriya cewa su yi watsi da haramcin da ya saka kan amfani da kuɗin na crypto tu a 2021.

Advertisement

CBN ya ce yadda ake yayin kuɗin na crypto yanzu a faɗin duniya ya nuna irin buƙatar da ake da ita ta saka dokoki a kan sa.

“A watan Fabarairun 2021 CBN ya haramta wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi amfani da cryptocurrency saboda almundahanar kuɗi da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci,” in ji sanarwar.

Advertisement

“Sai dai kuma, abin da ke faruwa a duniya ya nuna cewa akwai buƙatar a kula da dukiyoyin hada-hada ta intanet wato Virtual Assets Service Providers (V/ASPs).”

Ya ƙara da cewa hukumar kula da hada-hada da hannayen jari za ta fitar dokoki da sharuɗɗan amfani da dukiyoyoin intanet ɗin.

Advertisement

Amma babban bankin ya jaddada haramcin yin kasuwanci, ko kuma mallakar asusun crypto ga bankunan kasuwancin su da kansu

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending