Connect with us

News

Yan Ta’addan Dake Kashe Musulmi Sune Ke Kashe Kirista A Nijeriya -Shehu Sani

Published

on

Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani

DAGA MUSLIM YUNUS ABDULLAHI 

Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani  ya ce ‘yan ta’addan da ke kashe Musulmi a jihohin Katsina, Borno, da Neja, su ne wadanda ke kashe kiristoci a Kudancin Kaduna, Benue, da Filato.

Advertisement

Sani ya ce ta’addanci ba shi da alaka da addini, inda ya kara da cewa suna bayan harin da aka kai musu ne kawai.

Tinubu Ya Amince Da Kamfanonin Jiragen Sama 3 Domin Jigilar Maniyyatan Aikin Hajjin Bana 

Ya baiyana hakan ne a Shafin sa na twitter,Shehu Sani ya rubuta cewa yan ta’addan da ke kashe Musulmi a Katsina, Zamfara, Borno, Yobe da Niger, su ne ‘yan ta’addan da ke kashe Kiristoci a Kudancin Kaduna, Benue da Filato; ta’addanci ba shi da fifikon addini.

Advertisement

Babu wani addini da ya amince da tayar da zaune tsaye a Duniya,don haka duka mutane daya ne masu kisan Kiristoci da musulmin Nijeriya.

Hakan na zuwa ne bayan wasu ‘yan ta’adda sun kashe mazauna wasu al’ummomi a kananan hukumomi uku na jihar Filato a jajibirin Kirsimeti.

Advertisement

A wani labarin kuma Tinubu Ya Amince Da Kamfanonin Jiragen Sama 3 Domin Jigilar Maniyyatan Aikin Hajjin Bana 

Babban Bankin Najeriya CBN ya sauya matsayarsa kan hada-hada da kuɗin intanet ko kuma cryptocurrency a ƙasar.

Advertisement

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma’a da ke umartar bankunan kasuwanci na Najeriya cewa su yi watsi da haramcin da ya saka kan amfani da kuɗin na crypto tu a 2021.

CBN ya ce yadda ake yayin kuɗin na crypto yanzu a faɗin duniya ya nuna irin buƙatar da ake da ita ta saka dokoki a kan sa.

Advertisement

“A watan Fabarairun 2021 CBN ya haramta wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi amfani da cryptocurrency saboda almundahanar kuɗi da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci,” in ji sanarwar.

“Sai dai kuma, abin da ke faruwa a duniya ya nuna cewa akwai buƙatar a kula da dukiyoyin hada-hada ta intanet wato Virtual Assets Service Providers (V/ASPs).”

Advertisement

Ya ƙara da cewa hukumar kula da hada-hada da hannayen jari za ta fitar dokoki da sharuɗɗan amfani da dukiyoyoin intanet ɗin.

Amma babban bankin ya jaddada haramcin yin kasuwanci, ko kuma mallakar asusun crypto ga bankunan kasuwancin su da kansu

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending