Connect with us

News

Ganduje Ya Raba Masarautun Kano Gida Biyar Ne Da Mugun nufi – Kwankwaso

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya yi zargin cewa magajinsa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya raba masarautar Kano da mugun nufi.

Tsohon Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da ya yi da manema labarin a jihar Kano

Advertisement

Mutum 10 Sun Rasu, 12 Sun Ji Rauni A Hatsarin Mota Jihar Jigawa

Sanata Kwankwaso wanda ya nada mataimakinsa Dr. Abdullahi Umar Ganduje a matsayin wanda zai gaje shi a zaben 2015 ya samu tsamin dangantaka tun a shekarar 2016.

A ranar 8 ga Mayu, 2019, tsohon gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya raba masarautun Kano gida biyar: Kano, Bichi, Karaye, Rano, da Gaya, inda aka nada sabbin masarautun a matsayin masu daraja ta daya.

Advertisement

A ranar 9 ga Maris, 2020, Gwamna Ganduje ya tsige Sarki Muhammad Sanusi II bisa zarginsa da laifin rashin biyayya, sannan kuma ya kore shi zuwa Awe a jihar Nassarawa kafin ya maka gwamnati kotu.

A yanzu haka wasu mutane sun yi ta kiraye-kirayen a mayar da Sanusi II a matsayin sarki.

Advertisement

A yayin hirar, Kwankwaso, wanda shi ne mai baiwa kuma ubangidan siyasar Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya ce har yanzu ba su tattauna batun masarautu biyar da Ganduje ya kafa ba. Idan bukatar haka ta taso, za su zauna su toshe magudanar ruwa da suka taso a raba Masarautar.

Kwankwaso, wanda ake zargin yana rike da Gwamnati ne ta bayan fage, ya ce ya san cewa lokaci zai zo da za su tattauna batun Masarautar, ko a zauna a matsayin daya ko a zauna a yadda suke, ko ma a ruguza su.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending