News
Mutum 10 Sun Rasu, 12 Sun Ji Rauni A Hatsarin Mota Jihar Jigawa
DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO
Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC), a Jihar Jigawa, ta tabbatar da mutuwar mutum 10, yayin da wasu 12 suka samu raunuka a wani hatsarin mota da ya rutsa da su a hanyar Ringim zuwa Dutse, a Karamar Hukumar Ringim a jihar.
Kakakin hukumar, Ibrahim Yahaya ne, ya tabbatar wa kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) faruwar lamarin a Dutse.
Yahaya, ya ce hatsarin ya faru ne tsakanin wata mota kirar Volkswagen Golf da wata mota kirar Toyota kirar bas a kauyen Gidan Garke da misalin karfe 12:30 na rana.
Rahotanni na nuni da cewa hatsarin ya auku ne lokacin da motocin biyu ke dauke da fasinjoji 22, suka yi karo da juna sakamakon gudun wuce kima.
Kakakin, ya ce jami’an hukumar, sun kai wadanda abin ya shafa zuwa babban Asibitin Ringim.
A cewarsa, jami’an ba su iya tantance lambobin motocin biyu ba saboda sun kone kurmus
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
