Opinion
Shin ƙarya, yaudara da cin amana ne manyan shika-shikan siyasa?
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Siyasa na ci gaba da samun ma’anoni da fassara iri-iri daga bakunan ‘yan Najeriya.
Watakila wannan baya rasa nasaba da yadda ‘yan siyasa ke bulla da munanan halaye da dabi’u musamman bayn sun ci zabe.
Kungiyoyin kwadago na shirin fito-na-fito da gwamnatin tarraya kan albashi
Ita dai siyasa na nufin hanyoyin da za a bi a samar da shugabanci, a kuma gudanar da shuganbanci na gari, kamar yadda dakta Sa’idu Ahmad Dukawa na Jami’ar Bayero da ke Kano ya bayyana.
Haka kuma siyasa na nufin hanyoyin da za a bi a samar da shugabanci, a kuma gudanar da shuganbanci na gari.
To sai dai al’ummar Najeriya musamman Hausawa na ganin siyasa a matsayin wadda ke kunshe da munanan siffofi, da suka hadar da karriya da cin amana da yaudara da munafurci da sauransu.
Daga cikin masu irin wannan ra’ayi har malaman addini, waɗanda a lokuta da dama ke alaƙanta siyasa da wadannan munanan siffofi.
Wanne ne ma ya sa mafi yawan malaman addini ke kokarin kaurace wa siyasar, saboda mummunan fahimt da ake ci gaba da yi mata musamman a yankin arewacin kasar.
Me Ya Sa ‘Yan Najeriya Ke Alakanta Siyasa Da Munanan Dabi’u?
To ko ke masana harkokin siyasa ke cewa game da wannan ikirari?
Farfesa Abubakar Kari, malami a jami’ar Abuja ya ce al’amura ne suka lalace shi yasa mutane suka fara yi wa siyasa mummnar fahimta musamman a Najeriya.
Amma ya ce siyasa ta fara gurɓacewa ne a baya-bayan nan a Najeriya, domin kuwa a baya ba haka abin yake ba, musamman lokacin siyasar neman ‘yancin kai da ma jamhuriya ta farko da ta biyu.
”Abin da ya sa kuma shi ne su waɗancan ‘yan siyasar na farko sun gina siyasar tasu ne kan aƙida da ci gaban ƙasa, sannan kuma ba a amfani da abubuwa da dama da a yanzu ake amfani da su , shi yasa al’ummar wancan lokaci suka yi amanna da siyasa”, in ji malamin jami’ar.
Ya ce amma sannu a hankali al’amura suka riƙa lalacewa, har sai da ya kasance jam’iyyu da ‘yan siyasa ba su da wata cikakkaciyar aƙida a ƙasar.
Dakta Sa’ida Ahmad Dukawa ya ce abin da ya janyo mutane ke bai wa siyasa wannan fassara shi ne yadda ‘yan siyasar ke bayar da hoton kansu ta hanyar halayyarsu, inda ma a wasu lokuta suka ambata da bakunansu.
”A wasu lokutan ‘yan siyasar da kansu ke cewa ai siyasa ba ta rabo da ƙarya da cin amana da yarfe da zamba da maguɗi da munafurci da yarfe da makamantansu”, in ji shi.
Masanin ya ƙara da cewa a wasu lokuta su ‘yan siyasar da kansu ke cewa, ”idan mutum yana so a tono asirin iyaye da kakanninsa to ya shigo siyasa”.
Dakta Dukawa ya kuma ce mafi yawan ayyukan ‘yan siyasar na nuni da ire-iren waɗannan ɗabi’u da halaye.
”Ba sa jin komai su yi alƙawari su saɓa, ba sa jin komai su yi rantsuwa a kan ƙarya, ba sa jin komai a ba su amana su ci”, in ji Malamin jami’ar Bayeron.
Yadda Ƙasashen Duniya Ke Kallon Siyasa
Dakta Dukawa ya ce a ƙasashen duniya da dama ma ana yi wa siyasa makamancin wannan kallo, musamman a wanna lokaci na dimokraɗiyya ƙasashe da dama haka ake kallon siyasa.
Ko’ina akan yi bi-ta-da ƙullin siyasa da zarge-zargen laifukan da suka shafi rashawa daga ɓangaren ‘yan siyasa, sai dai kawai bambancin hukunci tsakanin ƙasashe.
”A wasu ƙasashen in an kama ɗan siyasa da laifi da wuri ake ɗaukar matakai a kansu, sabanin wasu ƙasashen da sai a daɗe ba a hukunta mutanen da aka kama da laifukan cin hanci ba”, in ji Dakta Dukawa.
Shi ma Farfesa Kari ya ce siyasa ta fara fita daga zukatan mutane a ko’ina cikin faɗin duniya sakamakon wasu munanan halaye da ‘yan siyasa ke aikatawa.
”Ko a Amurka idan ka lura za ka ga cewa idan aka yi zaɓe mutanen da ke fitowa domin kaɗa ƙuri’unsu ba su kai rabin al’ummar ƙasar ba, wannan kuma ba ya rasa nasaba da irin dawo daga rakiyar ‘yan siyasa da al’umma ke ci gaba da yi”, in ji shi.
