Connect with us

News

Bankin Ci-gaban Afirka zai bai wa wasu jihohin Nijeriya dala miliyan 540 domin bunƙasa ayyukan noma

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Bankin Ci-gaban Afirka (AfDB) zai bai wa wasu jihohin Nijeriya tallafin dala miliyan 540 domin bunƙasa ayyukan noma.

Bankin zai ware kuɗaɗen ne ga jihohi bakwai domin soma shiri na musamman kan bunƙasa fannin noma na yankin wato ”Agro-Industrial Processing Zones” (SAPZs) kamar yadda mai magana da yawun bankin na AfDB Banji Oyelaran-Oyeyinka ya bayyana a cikin wata sanarwa.

Advertisement

An Yi Nasarar Gano Wasu Matafiya Su 9 Da Suka Yi Ɓatan Damo

Oyelaran-Oyeyinka ya ƙara da cewa shirin na SAPZ zai mayar da hankali a kan manoman da ke yankunan karkara.

Kazalika ya bayyana cewa maƙasudin bankin na AfDB shi ne tallafa wa hada-hadar ayyukan noma da ɗorewar masana’antu a Nijeriya.

Advertisement

Oyelaran-Oyeyinka ya yi kari da cewa tallafin zai taimaka wa ƙasar wajen yaƙi da matsalar ƙarancin abinci.

 

Advertisement

TRT Afrika

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending