News
Da Naira Za A Dinga Biyan Kuɗaɗen Waje Da Aka Tura Najeriya
DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO
Daga yanzu, dukan kuɗaɗen ƙasashen waje da aka tura zuwa Najeriya ta hanyar kamfanoni masu hada-hadar kuɗi na ƙasa-da-ƙasa (IMTOs) za a riƙa biyan masu su da naira ne.
Wannan na cikin wasu sababbin ka’idojin da babban bankin Najeriya (CBN) ya fitar ne na baya-bayan nan.
Yadda Beraye Suka Tilasta Wa Manoma Kwana A Gonakinsu A Jihar Kano
Wasu daga cikin kamfanonin da abin ya shafa sun haɗa da Western Union, MoneyGram, Rapidtransfer, Ria, da sauran IMTOS da bankin na CBN tya amince da su, kamar yadda wata sanarwa da bankin Ecobank Nigeria ya fitar.
Abin da Sanarwa ta ce:
“Muna so mu jawo hankalinku kan sauye-sauyen tsarin da suka shafi hada-hadar kudaɗe na duniya zuwa Najeriya ta hanyar Western Union, MoneyGram, Rapidtransfer, Ria, da sauran IMTOS da babban bankin Najeriya (CBN) ya amince da su.
“Ka’idar da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya fitar mai kwanan wata 31 ga watan Janairu, 2024, ta nuna cewa duk kuɗin da ake turawa Najeriya (ta hanyar IMTOS da aka ambata a sama) za a biya su ne kawai da takardun kuɗi na Naira ta hanyar asusun banki ko ta amfani da tsabar kuɗi, dai-dai adadin da ake samu a kasuwar canji a Najeriya.”
Sanarwar ta kuma yi nuni da cewa kudaden da ke kasa da dala 200 ne kawai za a iya biyan su a cikin tsabar kudi a naira. Duk wani adadin sama da $200 za a biya a asusun banki.
“Bugu da ƙari, canja wurin da ya wuce Naira kwatankwacin dala 200 dole ne a sanya shi a asusun banki. Biyan kuɗin Naira wanda ya yi daidai da adadin kuɗin da ke ƙasa da $200 zai buƙaci tantancewa.”
An kuma lura cewa hanyoyin da aka amince da su na tantancewa don biyan kuɗi sun haɗa da lasisin tuki da fasfo na ƙasa da ƙasa da katin shaidar ɗan ƙasa da katin zaɓe na dindindin na INEC (PVC).