Connect with us

News

Da Ɗumi-ɗumi: Tsohon Gwamnan Kwara Ya Faɗa Komar Hukumar EFCC

Published

on

Tsohon Gwamnan Jihar Kwara State, Abdulfatah Ahmed

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

Tsohon Gwamnan Jihar Kwara State, Abdulfatah Ahmed, ya faɗa a komar Hukumar EFCC bisa zargin almundahana biliyoyin Naira a lokacin mulkinsa.

News Point Nigeria ta rawaito cewa, an ga lokacin da Ahmed ya isa ofishin EFCC na Ilorin da safiyar ranar Litinin.

Advertisement

Hukumar Hisbah a Kano ta musanta labarin da ake yada wa kan murabus din kwamandan ta Sheik Aminu Ibrahim Daurawa

Majiyar ta tamu ta ƙara da cewa EFCC ta gayyaci tsohon gwamnan ne don amsa mata tambayoyi dangane da yadda ya kashe kuɗaɗen da ake ya wawushe a lokacin mulkinsa a jihar.

 

Advertisement

Ahmed ya yi gwamnan Kwara ne daga 2011 zuwa 2019 inda ya miƙa mulkin jihar ga Abdulrahman Abdulrazaq.

 

Advertisement

Ko a shekarar 2021 EFCC ta gayyaci Ahmed ɗin zuwa babban ofishinta da ke Jabi a Abuja bisa zargin alaƙarsa da badaƙalar karkatar da Naira biliyan 9 daga asusun Hwnatin Kwara.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending