Connect with us

News

Wasu Yan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin ‘Yan Sanda A Zamfara

Published

on

DAGA MARYAM BASHIR MUSA 

 

Advertisement

Yan bindiga sun kashe dan sanda a harin da ’yan ta’addan suka kai a Babban Ofishin ’Yan Sanda da ke Karamar Hukumar Zurmia Jihar Zamfara.

Rahotanni daga jihar sun nuna cewa baya ga dan sandan da ya kwanta dama, maharan sun kashe wasu mutum shida da ake tsare da su a ofishin ’yan sandan.

Advertisement

Hukumar NiMet Ta Yi Hasashen Cewa Za A Yi Lullumi Na Tsawon Kwanaki 3 A Wasu Jihohin Kasar Nan.

 

Mazauna garin Zurmi sun ce a yammacin ranar Lahadi ne dandazon maharan suka kutsa cikin garin inda kai-tsaye suka wuce zuwa ofishin ’yan sanda, suka bude wa jami’an da ke bakin aiki wuta.

Advertisement

Ana zargin harin na daukar fansa ne saboda ’yan banga sun kashe wasu ’yan bindiga biyu a garin.

Kakakin ’yan sandan jihar Zamfara, ASP Yazid Abubakar, ya tabbatar da harin, inda ya kara da cewa an tura karin jami’an tsaro zuwa yankin, kuma kura ta lafa.

Advertisement

Rundunar ’yan sandan jihar ta kuma lashi takobin kamo wadanda suka yi wannan ta’addancin a garin Zurmi.

Karamar Hukumar Zurmi na daga cikin yankunan Jihar Zamfara da ke sansanonin ’yan bindiga.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending