News
Duk Da Tsadar Wutar Lantarki An Gaza Wadata ‘Yan Najeriya Da Hasken Wutar
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Mako guda bayan karin kudin wutar lantarki a wasu sassan Najeriya kamfanonin rarraba wutar sun gaza bayar da wutar da suka yi alkawari ta tsawon sa’o’I 20 zuwa 24.
Rahotanni na nuni da cewa cikin mako daya tak, kamfanonin su wallafa takardar ban hakuri ga jama’ar da ke zaune a yankunan da ake bayar da wutar ta tsahon sa’oi 20 zuwa 24 har sau 37 a shafukan su na Internet.
Jam’iyyar APC Da PDP, Duk Kanwar Ja Ce — Rabi’u Musa Kwankwaso
Gwamnatin Najeriya dai ta yi karin kudin wuta a wasu sassa daga naira 68 zuwa naira 225, wato ninkin sama da kaso 300 kenan.
To sai dai kuma tun kafin karin yaje ko ina aka fara samun matsaloli, daga bangaren kamfanonin rarraba wutar lantarkin a inda suka kasa cika alkawarin samar da wutar awanni 20 zuwa 24 kowacce rana.
