Connect with us

News

Manyan jami’an sojin Nijeriya 29 sun yi murabus

Published

on

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

A ranar Juma’ar da ta gabata wasu Janar-janar na sojin Nijeriya 29 suka yi murabus daga aiki a barikin soji da ke Jaji, Jihar Kaduna.

Channels ta ruwaito cewa 19 daga cikinsu Manjo-janar ne, yayin da 10 ke da muƙamin Birgediya-Janar.

Wasu Daliban Jami’ar Tarayya Ta Lokoja Sun Yiwa Malamin Su Zigidar A Harabar Makarantar 

Daga cikin jami’an da lamarin ya shafa har da Manjo Janar Victor Ezugwu, wanda ya wakilci takwarorinsa wajen yin jawabi.

Da yake jawabin, Victor ya ce yaƙi da ‘yan ta’adda zai zo ƙarshe ne idan aka ƙarfa wa dakaru salon yaƙin dare da sauransu.

Ezugwu ya yi kira ga manya da ƙananan sojojin da ke bakin aiki da su ƙara himma wajen yaƙi da maƙiya.

Advertisement

Haka nan, ya yi kira ga waɗanda za su gaje su da su nuna ƙwazo tare da yi wa ƙasa aiki tuƙuru fiye da wanda su suka yi.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending