Connect with us

News

An Kama Wani Mutum Da Bam A Banki A Jihar Plateau

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

An kama wani mutum da har yanzu ba a bayyana sunan sa ba da bam a jikin sa ya shiga harabar wani banki da ke garin Dadin Kowa a yankin Jos ta Kudu a jihar Plateau.

Advertisement

Jaridar PUNCH  ta ruwaito cewa nan take aka gano bam a jikin mutumin, inda cikin gaggawa aka fallasa shi kuma nan take jami’an tsaro suka rike shi domin kaucewa afkuwar wani bala’i.

 Matasa Na Da Rawar Takawa A Dukkanin Bangarori Na Cigaban Najeriya —Kwamared Ibrahim Salihu

Kamar yadda wani mai sharhi kan harkokin tsaro Zagazola Makama ya fitar a yau Talata a shafin sa na X, ya ce jami’an tsaron bankin me su ka yi tamaza su ka dakile harin lokacin da suka hango wanda ake zargin.

Advertisement

Wasu fusatattun mutane sun zo kan wanda ake zargin, inda su ka nemi da a kashe shi.

Daga baya an mika wanda ake zargin ga ‘yan sanda domin gudanar da bincike.

Advertisement

Hoton da ke makale a shafin Makama ya nuna mutumin da bam din a ɗaure a jikin sa.

Sai dai babu tabbas ko wanda ake zargin yana da alaka da wata kungiyar ta’addanci a kasar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending