Connect with us

News

 Matasa Na Da Rawar Takawa A Dukkanin Bangarori Na Cigaban Najeriya —Kwamared Ibrahim Salihu

Published

on

ƙungiyar ɗalibai ta unguwar Kurna wato Kurna Students Association, Kano, Kwamared Ibrahim Salihu

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Wani Ɗalibi a jami’ar Kimiyya da fasaha da ke garin Wudil a jihar Kano, kuma shugaban ƙungiyar ɗalibai ta unguwar Kurna wato Kurna Students Association, Kano, Kwamared Ibrahim Salihu ya bayyana cewa Matasa na da rawar takawa a dukkanin bangarori na cigaban Najeriya.

Advertisement

Kwamared Ibrahim Salihu ya bayyana hakan ne a wani sako da ya turawa da Jaridar Inda Ranka.

Wa’adin Awa 24: Za A Rushe Shaguna 500 A Abuja

Kwamared Ibrahim ya ce muddin idan matasa su ka haɗa kan su waje guda kuma su ka jajirce to babu shakka za su iya samar da shugabanci a dukkanin matakai a Najeriya.

Advertisement

Haka kuma shugaban ɗaliban ya yi kira ga matasa akan su guji siysar Daba ko Jagaliya da maula da kuma tumasanci domin hakan ne zai kai su ga samun yan tacciyar rayuwa abar misali.

Hakazalika, Kwamared Ibrahim din ya ce ya kamata matasa su yi koyi da rayuwar marigayi Malam Aminu Kano, domin cike ta ke da darussan rayuwa da zai amfani matasan idan su ka kwaikwaya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending