Connect with us

Politics

Ka Tsame Hannunka Shiga Sabgar Siyasar Kano Za Ta Janyo Maka Matsala  — Buba Galadima Ya Gargadi Shugaba Tiubu.

Published

on

Spread the love

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Jigon Siyasar Kano Buba Galadima, ya gargadi Shugaba Bola Tinubu kan yin katsalandan a siyasar Jihar Kano.

Advertisement

A wata hira da yayi da gidan Talabijin na ARISE, Galadima ya yi gargadin cewa idan shugaban kasa bai yi hankali ba siyasar Kano za ta iya ruguza shi.

Yau Shekaru 25 da rasuwar fitaccen mawamin Hausa mamman shata

Jigon jam’iyyar ta NNPP ya ce “Ya kamata Gwamnatin Tarayya da Shugaban ƙasa Bola Tinubu su yi taka-tsan-tsan da siyasar Kano, domin za ta iya ruguza shugabancinsa.

“Ina so in gaya wa Gwamnatin Tarayya ciki har da abokina Shugaba Bola Tinubu cewa ya kamata ya kula da siyasar Kano saboda irin tasirin da take da shi a siyasar Najeriya”.

Advertisement

Ba su taba yarda da abubuwan da muke faɗa ba, amma kuma Ni ina da masaniyar yadda muka yi da batun shawo kan dambarwar siyasar Kano a lokacin jam’iyyar NPN lokacin ina Shugaban Matasa.

Na san wasu manyan ‘yan siyasa a Kano ciki har da wasu attajirai da suka zo ganawa da Shugaban ƙasa cewa ya tsige Abba Yusuf kawai babu abin da zai faru.

Mutumin da ya faɗi haka ya kamata wayonsa ya wuce haka da har zai faɗi cewa babu abin da zai faru, amma ka tambaye su ta yaya aka yi ba ka ci zabe tun farko ba”.

Advertisement

Galadima ya yi magana ne bayan Sanata Rabi’u Kwankwaso Shugaban NNPP na kasa ya zargi Gwamnatin Tarayya da sauraron wasu mutane da basa son cigaban Kano kan rikicin masarautu.

Dukansu Alhaji Muhammadu Sanusi da Alhaji Aminu Ado Bayero suna da’awar sarautar Sarkin Kano.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tsige Ado Bayero ne tare da umartar shi da ya fice daga fadar, amma Sarkin Kanon na 15 ya yi watsi da umarnin nasa inda ya garzaya kotu tare da komawa karamar fada da ke Nassarawa.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *