News
Shiru Bazai Haifar Da Ɗa Mai Ido Ba A Rikicin Da Akeyi Na Samun Jigo A Kano – —Umar Ardo, Ph.D
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Naji matukar rashin jin dadi game da rikicin jigo da yake faruwa a jihar Kano. Kuma ko wane Mai tunani dan Arewa zai ji ba dadi shima. Nakuma ji rashin dadi musamman akan yan siyasar kano wanda duk akansu na dora laifin, kan
karkatattun hukuncin ra’ayoyinsu da suka shafi gwamnati da siyasa baki daya, Wanda duk su suka haifar da wannan yanayi da ake ciki a halin yanzu.
Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero Ya Daga Tuta A Fadar Nassarawa
A lokaci irin wannnan na cigaba a arewacin Najeriya, musamman akan asalin Samar da kalifa, Wanda akan hada hannu da karfe dan a fadakar da mutane wajen bin akidar hadaddiyar kungiyar sarakuna domin samun cigaba acikin al’umma Wanda Kuma zai kawo hadin kai a cikin al’umma ta bangaren al’adu, siyasa, tattalin arziki a tsasarance cikin dukkanin jihohin Najeriya.
Domin nuna karfin amfanin da al’ada take dashi Wanda ya samo asali tun kaka da kakanni yake Kuma warware abubuwa ta fannin siyasa, tattalin arziki, da kuma abun da ya shafi matsalolin zamantakewar al’umma.hakan yanasa a samu fatan amincewa da al’adun gargajiya domin a sake jaddada jigon ma’aikatun gargajiya wajen Samar da hadin Kan jama’a da ra’ayoyinsu a jerin al’adummu daban daban. Wandanda zasuyi amfani a cikin al’umma ta hanyar magance matsalolin mulkin dimokaradiya, akumayi aiki da mutane ta hanyar gaskiya domin samun tarihi mai Jaruman al’umma.
-Abintakaici a irin wannan mawuyacin halin rashin kishi, izza, jahilci ake aiki da abinda bai daceba wajen fifita siyasa, wasu yan San Kai da suke a tsakiyar siyasa nasan karyar da karfin kalifanci da aka kikira a matsayin mafi karfin masarautu, sai ma Kara wahalar da mawuyacin yanayin da ake ciki na rashin tabbas da Arewa take fuskanta a yanzu na hanyar mulkin dimokaradiya.
Don haka, babu wani dan kalifanci, ko kadan daga cikin masu rike da mukaman manyan yan siyasar kano, da ya kamata a ga yana cikin wannan tada zaune tsaye a cikin al’umma. dole ne duk yan ƙasa masu kishin kansu su yi Allah wadai da shi.
Saboda haka nawa la’akarin shi ne dukkan yan siyasar da suke haifar da wannan cece kucen a masarautar Kano nan take su janye hannunsu a ciki su Kuma nesanta kansu daga wani abu daya shafi ciki da wajen masarauta, su Kuma bada kwakkarar gudummuwarsu da za’a gyara matsalolin yan Arewa da mutanen su, Wanda zai kawo cigaba da hadin kai, jituwa, mutunci da wadata a Najeriya
A karshe, ina kira ga Mai Martaba Sarkin Musulmi, a matsayinsa na shugaban masarautar kalifanci, da ya gaggauta kiran taron Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Arewa, domin tattaunawa a kan lamarin, tare da shawartar duk wanda abin ya shafa, ta yadda za a samu mafita mafi dacewa .
Don shuwagabannin gargajiya sun yi shiru da jajircewa kan lamarin Wanda bazai haifar da da Mai Ido ba. A haƙiƙa, zai zama abin kunya da tozarci ga su kansa al’ummar gargajiya, inda a ke nuna ma’aikatan da suka mamaye makarantar a matsayin marasa tasiri kuma gadonsu da kimarsu ba su da amfani wajen magance hatta matsalolin hukumomin nasu a cikin al’ummar wannan zamani.
Kamar yadda na bayyana a sama, kirkirar kalifanci ita ce laima da ke ba mu fakewa baki daya, Gado ne kuma abin alfaharinmu, don haka ba za mu iya ba kuma bai kamata mu zauna mu kalli yunƙurin da ake yi na ruguza dacewa da daukakarsa take da shi ba.
