News
Hukumar Sufurin Jiragen Sama NCAA Ta Dakatar Da Jerin Jiragen Alfarma 10 Daga Yin Shawagi A Najeriya
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Hukumar Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) ta dakatar da wasu jiragen kashin kai guda 10 daga yin shawagi a kasar.
Rahotanni na nuni da cewa jerin kamfanonin jiragen alfarman da NCAA ta dakatar:
Ƙarin kuɗin ruwa zuwa kashi 30 bisa 100 da CBN ya na hana masana’antu ɗaukar ma’aikata —Dangote
Azikel Dredging Nigeria Ltd
Bli-Aviation Safety Services
Ferry Aviation Developments Ltd
Matrix Energy Ltd
Marrietta Management Services Ltd
Worldwide Skypaths Services
Mattini Airline Services Ltd
Aero Lead Ltd
Sky Bird Air Ltd
Ezuma Jets Ltd.
Daraktan hulda da jama’a na NCAA, Michael Achimugu, ya sanar cewa hukumar ta tura jami’ai zuwa rumfunan kamfanonin da umarnin ya shafa domin sa ido kan su.
NCAA ta soke lasisin jiragen ne saboda sun ki bin umarninta na zuwa a tantance su da kuma sabunta takardunsu.
Hukumar ta umarci jiragen kashin kai su sabunta takardu ne bayan bincike ya gano cewa wasunsu na daukar fasinjar haya domin samun kudade.
A kan haka ne ta ba umarce su su su sabunta takardu a kuma tantance kafin ranar 19 ga Afrilu, 2024.
Dokar hukumar dai ta haramta harkar hayar fasinja ko dakon kaya ko sakonni ga jiragen kashi kai a kasar.
