News
Matatar Man Dangote Ta Zargi Hukumar NURPC Da Gazawa Wurin Gudanar Da Ayyukanta
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Matatar man Dangote ta yi kira ga hukumomin Nijeriya da su tursasa wa kamfanonin da ke haƙo mai a Nijeriya su bi dokar man fetur ta Nijeriya wadda ta buƙaci su rinƙa aika wa matatun mai na cikin ƙasar fetur.
Matatar Man Dangote ta koka kan cewa rashin hakan na ja musu asara.
Gwamnatin Tarrraya Ba Ta Rabawa Jihohi Naira Biliyan 570 Ba – Gwamnan PDP Ya Musanta Tinubu
Matatar man ta Dangote wadda ke iya samar da ganga 650,000 a duk rana wadda shahararren mai kuɗin nan na Afirka Aliko Dangote ya gina a wajen Legas kan dala biliyan 20, na ta gwagwarmaya wurin ganin ta samu isashen mai daga Nijeriya.
A wata sanarwa da matatar man ta Dangote ta fitar a ranar Juma’a, ta zargi hukumar da ke sa ido kan bin dokokin harkokin man fetur ta Nijeriya NURPC da gazawa wurin aiwatar da dokokin samar da ɗanyen mai ga matatun cikin gida.
“Damuwarmu a kullum ita ce NUPRC na ta bi, amma kamfanonin mai na ƙasa da ƙasa ba su bin umarni,” in ji Anthony Chiejina, wani mai magana da yawun Dangote a wata sanarwa da ya fitar.
“Don haka, sau da yawa muna sayen danyen mai na Nijeriya daga ‘yan kasuwa na duniya a kan ƙarin $3- $ 4 a kan kowace ganga wanda ke nufin an samu ƙarin dala miliyan uku zuwa huɗu a kan kowane jirgin ruwa na mai.
Matatar tace tana sa ran za ta karbi jiragen ruwa na mai 15 a watan Satumba wanda a ciki NNPC ta bayar da shida.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
