News
Jami’a 1 Tal Ce Ta Iya Shiga Jerin Jadawalin Manyan Makarantu 1000 Na Duniya A Najeriya
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Jami’o’in Najeriya sun gaza shiga jerin jadawalin manyan makarantu 1000 na duniya a jere na tsawon shekaru 3 kamar yadda Mujallar Times Higher Education ta ƙasar Burtaniya ta wallafa.
A jadawalin shekarar 2024, an samu jami’o’i biyu – jami’ar Covenant da ke jihar Ogun da jami’ar jihar Ibadan – da suka shiga jerin manyan makarantu 1000 na duniya.
Sannan a shekarar 2023 kuwa an samu jami’o’i uku da suka shiga wannan jeri da suka haɗa da: Jami’ar Ibadan (UI), da Jami’ar Legas (UNILAG) Jami’ar Covenant.
An Gurfanar Da Wanda Zai Kashe Kansa Saboda Yan Uwansa Sun Ki Taimaka Masa A Kotu
Sai dai a jadawalin shekara mai zuwa ta 2025, Jami’a ɗaya ce ta kai bantenta, wato Jami’ar Covenant. Wannan jami’a mai zaman kanta ita ce tilo ta shafe tsawon lokaci tana shiga wannan jadali har ma a shekarar 2019.
A cikin manyan jami’o’in Najeriya baya ga Jami’ar Covenant, Jami’ar da ke biye da ita, ita ce Jami’ar Ahmadu Bello wacce ta zo ta 1001.
sauran Jami’o’in da suka sauran da suka take wa waɗannan jami’o’i baya su haɗa da: Jami’ar Bayero da Jami’ar Fasaha ta Akure da Jami’ar tarayya ta fasaha da ke Minna, sai Jami’ar Benin da Jami’ar Ilorin.
Game da manyan jami’o’in da ke kan gaba a wannan jadawali kuwa, Jami’ar Oxford ita ce ta cigaba da riƙe kambunta a matsayin ta ɗaya na tsawon shekaru. Wannan na zuwa ne saboda cigaban da take samu a fannin kuɗin shigar ta daga masana’antu da yawan masu amfani da kundaye da maƙalun bincike da kuma ingancin koyarwarta.
Makarantar Fasaha ta Massachusetts (MIT) ta ƙasar Amurka wacce ta matsa da taku ɗaya, inda ta zama ta biyu jerin jadawalin.
Uku ita ce jami’ar Harvard ta ƙasar Amurka, sai dai ita kuma Jami’ar Stanford faɗowa ta yi daga matakinta na biyu zuwa ta shida kuma mafi girman faɗuwar darajarta tun shekarar 2010.
Mujallar Bibiyar Manyan Makarantu ta ce an fidda wannan jadawali ne ta la’akari da abubuwa uku: Bincike da koyarwa da kuma tasirin karatun.
Ta ce warwara kuwa, za a iya kasa matakan da ta bi zuwa – Koyarwa (kyawun muhallin karatu) Bincike (Yawansa, kuɗin shiga da ƙimarsa) da ingancin bincike (gudunmowar binciken, ƙarfin binciken da lambar yabon bincike da tasirinsa) da Ƙimar Jami’ar a Duniya (ma’ikata, ɗalibai da bincike) da Kafuwarta (kuɗin shiga da Iyaye).
Inagancin bincike yana ɗaukar kaso 30% sai yanayin muhallin wurin bincike kaso 29%. Koyarwa kuwa na ɗaukar kaso 29.5% , sai ƙimar Jami’ar a idon duniya kaso 7.5%. Sannan gudunmowar jami’ar wajen ciyar da masana’antu da dabarun ƙirƙire-ƙirƙire da sabunta tunani da shawarwari na ɗaukar kaso 4%.
