Connect with us

News

Gwamnatin Jihar Kano Ta Kaddamar Da Rigakafin Cutar Shan Inna

Published

on

img 20241102 wa00732974746794567520589

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA

Gwamnatin jihar Kano a karkashin ma’aikatar lafiya, ta kaddamar da rigakafin cutar shan inna a karamar hukumar Ungogo, saboda yawan al’ummar yankin da kuma tarihin bullar cutar.

Advertisement

Dokta Abubakar Labaran yusif, ya bayyana dalilin kaddamar da rigakafin cutar shan inna a kamar Hukumar Ungogo, ya ce karamar hukumar na da adadin yara masu yawa

Bayan Hukuncin CAF An Fara Kamen ’Yan Najeriya A Kasar Libya

Ya kara da cewa  Ungogo na fuskantar barkewar cututtuka masu yaduwa kamar kwalara da cutar Mashako.

Advertisement

A nasu jawabin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) sunusi mayana ta nuna damuwarta kan yadda cutar shan inna  ke ci gaba da wanzuwa.

Dakta Mayana, ta yi jawabi ne a taron gangamin yaki da cutar shan inna ta 0 a karamar hukumar Ungogo, ta sha alwashin fadada hanyoyin da za a wayar da kan jama’a domin kawar da cutar.

Advertisement

“Muna kashe makudan kudade domin ganin an kawar da wannan cutar amma abin mamaki duk shekara muna yin wannan gangami amma ba mu cika sharuddan da ake bukata ba, don haka a wannan karon a shirye muke mu yaki wannan cutar ta Shan Inna ba tare da gajiyawa ba don ganin cewa Kano ta samu ‘yanci.

Alh Abdulkadir magajin malam hakimin karamar hukumar Ungogo ya yi kira ga iyaye da su fito da ‘ya’yansu domin karbar allurar rigakafin cutar.

Advertisement

Sai dai ya yabawa gwamnatin jiha karkashin jagorancin Engr Abba kabar yusif bisa kokarin da yake yi na magance cututtuka masu yaduwa da marasa yaduwa.

Jihar na da burin yi wa yara miliyan 3.6 allurar rigakafin shekaru kasa da shekaru 5 a fadin kananan hukumomi 44.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending