Connect with us

News

Gwamnatin Tarayya Ta Roƙi Chadi Kada Ta Janye Daga Cikin Ƙasashen Dake Yaƙi Da Boko Haram

Published

on

Gwamnatin Tarayya Ta Roƙi Chadi Kada Ta Janye Daga Cikin Ƙasashen Dake Yaƙi Da Boko Haram

DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO 

Shugaban kasa  Bola Ahmed Tinubu ya tura wata tawaga mai ƙarfin gaske zuwa N’Djamena, babban birnin Chadi bayan da Shugaban Chadin ya yi barazanar janye dakarun ƙasarsa daga rundunar haɗaka ta yaƙi da ‘yanta’adda a yankin Sahel.

Advertisement

A jiya Lahadi ne tawagar ta Najeriya ta je N’Djamena, inda a can hedikwatar rundunar (MNJTF), da ta ƙunshi dakarun Najeriya da Nijar da Chadi da Kamaru da kuma Jamhuriyar Benin.

Shugabannin ƙungiyar ƙasashen G20 sun hallara a kasar Brazil

Shugaba Deby ya yi barazanar janye sojojin ƙasarsa ne bayan da mayaƙan da ake zargi na ƙungiyar Boko Haram ne suka kashe dakarun ƙasarsa 40 a tsibirin Barkaram, da ke yankin tafkin Chadi a ranar 27 ga watan Oktoba.

Advertisement

Saboda wannan barazana ne shugaban na Najeriya ya tura tawagar ƙarƙashin jagorancin mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, domin tattauna batun haɗin kan tsaron.

Rahotanni sun ce, bayan gabatar da ta’aziyyar Shugaba Tinubu ga Shugaban na Chadi kan rasa sojojin, tawagar ta tabbatar wa da shugaban na Chadi samun cikakken goyon bayan Najeriya wajen yaƙi da ta’addanci.

Advertisement

Babban hafsan hafsoshin Najeriya Janar Christopher Musa, wanda shi ma yake cikin tawagar ya ce ƙudurin sojin ƙasashen biyu zai tabatar da nasarar yaƙi da ‘yanta’adda.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending