News
Yan Sanda Sun Kama Wata Mota Ɗauke Da Ƙananan Yara 59 Da Ake Zargin Sato Su Aka Yi
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta kama wasu yara maza 59 da ake zargi anyi safarar su ta hannun ‘yan sintiri da masu gadi
Kwamishinan ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, Olatunji Disu, ya bayyana cewa an gano yaran masu shekaru tsakanin 4 zuwa 12 ba tare da cikakkun takardu ko amincewar iyaye ba.
Jaridar KANO TIMES ta ruwaito cewa lamarin da ya haifar da fargabar cin zarafin yara da safarar su.
“A ranar 6 ga watan Janairun 2025, da misalin karfe 15 : 30, wata tawaga karkashin jagorancin mataimakin Sufeton ‘yan sanda (DSP) Sarki Umar ta tare wata farar motar kirar Peugeot 15 tare da Reg. No. KMC 283 ZJ a kan hanyar Abuja zuwa Kano.
“An gano motar bas din tana jigilar yara maza 59 masu shekaru tsakanin 4 zuwa 12. Binciken farko ya nuna cewa yaran da suka fito daga iyalai daban-daban, wani mutum mai suna Idris Usman, mazaunin jihar Nasarawa ne ke jigilar su. Ya yi tattaki zuwa jihar Kano ne domin tara yaran kan hanyar zuwa jihar Nasarawa da nufin horar da su,”
Rundunar ‘yan sandan ta baiwa jama’a tabbacin gudanar da cikakken bincike a kan lamarin domin gano cikakken aikin da kuma tabbatar da tsaron yaran.
