News
Gwamnatin Kano Ta Kulla Alakar Ceto Matasa Daga Harkar Shaye-shaye Da Zaman Kashe Wando
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf Kulla Alakar ceto matasa daga harkar shaye-shaye da zaman kashe wando da ke fadin jihar tare da ba su damar samun kyakkyawar rayuwa ta hanyar ilimi da cigaba.
Hakan na kunshe a Lokacin mai ba wa Gwamna shawara a fannin matasa da wasanni, Hon. Sani Musa Danja, ya kai ziyara Jami’ar Sheikh Khalifa Isyaka Rabiu (KHAIRUN) domin kulla alakar bawa matasa ilimi cikin sauki.
ASSOMEG Zata Hada Kai Da Gwamnatin Kano Dan Inganta Ayyuka Sama Da 300
Wannan ziyara na daya daga cikin matakan da gwamnatin Jihar Kano ke dauka domin tabbatar da an ceto matasa daga illolin shaye-shaye da zaman kashe wando, tare da ba su damar samun kyakkyawar rayuwa ta hanyar ilimi da cigaba.
A lokacin ziyarar, Sani Musa Danja ya bayyana cewa, wannan tsari wani bangare ne na kudirin Gwamna Abba Kabir Yusuf na samar da hanyoyin da za su tallafa wa matasa wajen samun ilimi cikin sauki da kuma taimakawa wajen bunkasa rayuwarsu ta fuskar kwarewa, ilimi da sana’o’i.
Haka kuma, ya jaddada cewa gwamnatin jihar na himmatuwa wajen ganin ta rage matsalolin da ke hana matasa cigaba, musamman harkar shaye-shaye, ta hanyar samar da mafita mai dorewa ta fuskar ilimi, wasanni, da horarwa.
Da yake karbar bakuncin tawagar gwamnatin, shugaban Jami’ar Sheikh Khalifa Isyaka Rabiu, ya jinjinawa kokarin gwamnatin jihar wajen tallafa wa matasa, tare da tabbatar da cewa Jami’ar za ta bayar da cikakkiyar gudummawa wajen cimma wannan buri.
An kammala taron da tabbacin kulla kyakkyawar alaka tsakanin gwamnatin Jihar Kano da Jami’ar domin tallafa wa matasa wajen samun ingantacciyar rayuwa da cigabamai dorewa.
