News
Matuƙa Motoci Sun Razana Bayan Ƴan Sanda Sun Fara Binciken Takardu
DAGA MAIMUNA RABIU UMAR
Hakan na zuwa ne a lokacin da rundunar ƴan sanda ta jaddada aniyarta ta tabbatar da bin dokar mallakar takardun inshora ga matuƙa motoci.
Sufeton ƴan sanda, Kayode Egbetokun ya bada umarnin, wanda an yi hakan ne don kiyaye dokokin hukumar inshora, kamar yadda Kakakinsa, Muyiwa Adejobi ya bayyana a wata sanarwa.
Ya ce kamar yadda suka alƙawuranta, za a fara binciken ne don ganin an kiyaye dokokin daga ranar 1 ga watan Fabrairun 2025 kamar yadda aka tsara.
Ya kuma ce duk wanda aka kama da laifin ƙin bin dokar, to za a hukunta shi, ya na mai kira a gare su da su kiyaye don guje wa tozarci.
Kazalika, ya nanata cewa har yanzu jami’ansu na cigaba da ƙoƙarin tabbatar zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Advertisements
