News
Rundunar ‘Yan Sanda Ta Kashe ‘Yan Ta’adda 7, Ta Kwato Makamai da Alburusai
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta samu gagarumar nasara a yaki da ta’addanci, inda ta hallaka ‘yan ta’adda bakwai tare da kwato makamai da kudaden fansa a hare-hare daban-daban da ta kai a sassa daban-daban na ƙasa.
A ranar 14 ga Fabrairu, 2025, jami’an ‘yan sanda a Jihar Kebbi sun bi sawun wasu masu garkuwa da mutane da suka sace wani mutum mai shekaru 60 a kauyen Gobiraje. A yayin musayar wuta, an kashe ‘yan ta’adda hudu, an kama guda ɗaya da raunuka masu tsanani, sannan aka ceto wanda aka sace ba tare da wata illa ba. Har ila yau, an kwato Naira miliyan uku (N3,000,000) da aka biya a matsayin kudin fansa.
An Tsinci Jariri A Cikin Kwali A Unguwar Tudun Murtala Tagarji A Kano
Haka kuma, a ranakun 8 da 9 ga Fabrairu, 2025, jami’an ‘yan sanda a Jihar Imo sun kai samame a sansanonin ‘yan ta’adda na IPOB/ESN. A wannan farmaki, an kashe shugabanni biyar daga cikinsu tare da kwato makamai da dama, ciki har da bindigogi kirar AK-47 da pump-action.
Babban Sufeton ‘Yan Sanda na Najeriya, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, ya yabawa jami’an da suka gudanar da wadannan hare-hare, tare da jaddada aniyar rundunar wajen kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa. Ya bukaci al’umma da su ci gaba da ba da hadin kai ga hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiyaa ƙasar.
