Connect with us

News

An Kama Ɗan Kasuwar Angola Da Hodar Iblis A Filin Jirgin Sama A Kano

Published

on

An kama ɗan kasuwar Angola da hodar iblis a filin jirgin sama a Kano

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) ta cafke wani ɗan kasuwa ɗan Angola, Mbala Dajou Abuba, mai shekaru 42, a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano, yayin da yake ƙoƙarin safarar hodar iblis zuwa ƙasar Turkiyya.

Advertisement

A cewar kakakin NDLEA, Femi Babafemi, an kama Abuba ne a ranar Talata, 25 ga Fabrairu, 2025, lokacin da yake shirin shiga jirgin Egypt Air MS 880 zuwa Istanbul ta hanyar birnin Cairo.

Rikici Ya Barke A Jihohi Da Dama Kan Aiwtar Da ‘Yancin Cin Gashin Kai Na Kananan Hukumomi

Bayan an yi masa gwajin jiki, an gano cewa ya haɗiye hodar iblis a cikin cikinsa, wanda daga bisani ya fitar da kwanson hodar iblis guda 120, masu nauyin kilogiram 1.829. Abuba ya bayyana cewa yana gudanar da kasuwanci a Angola kafin ya tsunduma cikin fataucin miyagun ƙwayoyi.

Advertisement

A wani samame makamancin haka, NDLEA ta kama wani ɗan kasuwa mai sayar da kayan gyaran mota, Okeke Ebuka Igwe, a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas, yayin da yake ƙoƙarin aika hodar iblis mai nauyin kilogiram 1.10 zuwa Angola.

Har ila yau, wani mutum mai suna Ezechi Iyke Cyprian an kama shi da hodar iblis mai nauyin kilogiram 5.40 a cikin motarsa ƙirar Toyota Sienna, yana ƙoƙarin jigilar ta zuwa Owerri, jihar Imo.

Advertisement

A tashar jiragen ruwa ta Tincan da ke Legas, jami’an NDLEA sun gano kwalayen tabar wiwi nau’in Canadian Loud guda 128 da aka ɓoye a cikin wata mota ƙirar Toyota Venza da aka shigo da ita daga Canada. An kama wanda ake zargi, Bamidele Joseph, mai shekaru 44, wanda yanzu haka yana hannun hukuma.

Hukumar NDLEA ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da yaki da masu safarar miyagun ƙwayoyi domin tabbatar da tsaro da lafiyar al’umma.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending