Connect with us

News

Rundunar Anty Snatching Phone Ta Kama Barayi Biyu Da Ake Zargi Da Ƙwace Wayoyi A Kano

Published

on

Rundunar Anty Snatching Phone ta Kama Barayi Biyu da Ake Zargi da Ƙwace Wayoyi a Kano

 

Rundunar tsaro ta Anty Snatching Phone da ke yaƙi da faɗan daba, ƙwacen waya da kuma daƙile shaye-shayen kayan maye a nan Kano, ta kama wasu matasa biyu da ake zargi da aikata laifukan sata da ƙwace wayoyi a yankunan Gaida da Ja’en.

Advertisement

Kwamandan rundunar, Inuwa Salisu Sharaɗa, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a, inda ya ce ɗaya daga cikin matasan an kama shi ne bayan an same shi da laifin tare masu baburan Adai-daita sahu tare da yi musu ƙwace a yankin Gaida, har ma ya yi yunƙurin farwa jami’an tsaron lokacin da suka zo kama shi.

Hukumar Hisba Ta Kulle Shagon Caca A Cikin Watan Ramadan A Kano 

Haka zalika, kwamandan ya ce sun kama wani matashi da ake zargi da shiga wani shagon Aski a Ja’en layin Shago Tara inda ya sace wayar mai shagon da aka kiyasta kudinta a Naira dubu 120, amma daga baya ya sayar da ita kan dubu 70.

Advertisement

A yayin da suke amsa tambayoyi, matasan sun bayyana nadamar su kan abin da suka aikata, inda suka ce hakan shi ne karo na ƙarshe da za su aikata irin wannan aika-aika.

Kwamandan ya tabbatar da cewa da zarar an kammala bincike, za a gurfanar da matasan a gaban kotu domin fuskantar hukunci.

Advertisement

Ya kuma sha alwashin ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace domin kawar da miyagun laifuka da ke addabar al’ummar Kano.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending