News
SERAP Ta Soki Ƙudirin Hukunta Masu Gujewa Zaɓe
Kungiyar kare haƙƙin ɗan-adam, SERAP, ta bukaci Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da Kakakin Majalisar Wakilai, Tajuddeen Abbas, da su janye ƙudirin da ke neman tasa ƙeyar waɗanda ba su yi zaɓe ba zuwa gidan yari na wata shida ko kuma su biya tarar N100,000.
A wata takarda da Mataimakin Daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare, ya fitar a ranar Asabar, kungiyar ta bayyana cewa matakin na majalisa ya sabawa doka kuma za su garzaya kotu idan ba a janye ƙudirin ba.
Shehu Sani Ya Yi Allah Wadai Da Kisan Gilla A Edo, Ya Bukaci Hukumomi Su Dauki Mataki
SERAP ta jaddada cewa dokar ƙasa ta bada ƴancin yin zaɓe amma ba tilas ba ne, kuma ƙudirin ya saɓa wa sassa da dama na kundin tsarin mulki, musamman doka ta 14(1)(c) da ke tabbatar da ƴancin shiga siyasa.
Kungiyar ta kuma bukaci a yi kwaskwarima ga dokokin zaɓe, domin bai wa ƴan kasa damar yin rajista da sauran al’amuran zaɓe ta yanar gizo, don sauƙaƙa tsarin dimokuraɗiyya.
