Connect with us

News

DA ƊUMI-ƊUMI: Pakistan Za Ta Dauki Fansa Kan Harin Sama Da India Ta Kai

Published

on

06pakistan 1 jblh mobileMasterAt3x

Aƙalla mutane bakwai ne suka rasa rayukansu, ciki har da yara ƙanana, sakamakon wani hari da India ta kai ta sama a wani yanki na Pakistan da daddare a jiya Litinin.

Rahotannin da gidan talabijin na gwamnati a Pakistan ya fitar sun bayyana cewa rundunar sojin ƙasar ce ta tabbatar da harin, inda ta ce India ta harba makamai masu linzami a wani yanki da ke arewacin ƙasar.

Advertisement

‘Yan Bindiga Na Cin Karensu Babu Babbaka A Shanono Da Bagwai  – Dan Majalisa

Baya ga mutanen da suka mutu, wasu da dama sun samu raunika, kuma jami’an agajin gaggawa na ci gaba da aikin ceto a yankin da abin ya faru.

Gwamnatin Pakistan ta bayyana cewa za ta dauki fansa a “lokaci da wuri da suka dace”, tana mai zargin India da keta hurumin ƙasar da kuma tayar da zaune tsaye.

Advertisement

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da dangantaka ke ƙara tsami tsakanin ƙasashen biyu da ke da makaman nukiliya, musamman a kan rikicin yankin Kashmir da ke janyo ce-ce-ku-ce tsakanin New Delhi da Islamabad.

Kawo yanzu dai babu wani jawabi daga hukumomin India dangane da harin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending