News
Indiya Ta Tabbatar Da Asarar Jiragen Yaƙi A Arangamar Da Ta Yi Da Pakistan
Rundunar tsaron Indiya ta tabbatar da cewa wasu daga cikin jiragen yakin ta sun fadi yayin arangamar da ta yi da Pakistan a farkon watan Mayu — tabbacin farko daga hukumomin kasar tun bayan barkewar rikicin.
Babban Hafsan Tsaro na Indiya, Janar Anil Chauhan, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake jawabi a taron Shangri-La Dialogue, babban taron tattaunawar tsaro da kasashen Asiya ke gudanarwa a birnin Singapore.
Shugaban Kasa Ya Tsallake Rijiya Da Baya Bayan Fashewar Tayar Jirgin Sama
Tun da farko dai, hukumomin Indiya sun dage kan cewa ba su yi asarar ko da jirgi guda ba a fadan da ya barke bayan wani hari da aka kai wa masu yawon bude ido a sashen Kashmir da Indiya ke iko da shi a watan Afrilu. Indiya ta zargi Pakistan da hannu a harin.
Ita kuwa Pakistan, ta shaida cewa ta harbo jiragen yakin Indiya har guda shida, ciki har da uku kirar Rafale daga Faransa — lamarin da ya tayar da jijiyoyin wuya a tsakanin kasashen biyu masu makaman nukiliya.
Lokacin da wakilin jaridar Bloomberg ya tambayi Chauhan dangane da wannan ikirari na Pakistan, sai ya fara musanta adadin, yana mai cewa, “wannan cikakken kuskure ne.”
Sai dai daga bisani ya sassauta harshe, yana mai cewa:
“Abin da ya fi muhimmanci shi ne dalilin da ya sa suka fadi,” — wata alama da ke nuni da cewa lallai akwai asarar jirage daga bangaren Indiya.
Kuskuren Dabara Da Sauya Salon Hari
Janar Chauhan ya kara da cewa sojojin Indiya sun yi “kuskuren dabara” a farkon arangamar.
“Mun fahimci inda muka yi kuskure, muka gyara, sannan muka sake aiwatar da dabarunmu cikin kwana biyu, muka koma kai hare-hare daga nesa,” in ji shi.
Wannan furuci ya kara tabbatar da cewa arangamar ba ta kasance da sauki ba ga Indiya, wanda hakan na iya zama darasi ga tsarin dabarun tsaro a gaba.
Tashin Hankali Tsakanin Kasashen Nukiliya
Fadan ya samo asali ne daga hare-haren da Indiya ta kai a yankin da Pakistan ke iko da shi a Kashmir — wanda ke kara nuna tsananin sabanin dake tsakanin kasashen biyu tun shekaru da dama da suka gabata.
Bayan kwanaki hudu na arangama, kasashen biyu sun sanar da tsagaita wuta a ranar 10 ga watan Mayu — abin da ya kawo ƙarshen fadan da ke barazanar rikidewa zuwa rikici mai girma tsakanin manyan makiyaya na Asiya
