News
Maƙabartar Kuka Bulukiya Ta Zama Mafakar ’Yan Daba a Cikin Birnin Kano

Wata maƙabarta mai tarihi a tsakiyar birnin Kano da ake kira Kuka Bulukiya, yanzu ta koma mafakar ’yan daba da masu aikata miyagun laifuka, lamarin da ke tada hankalin mazauna yankin da masu amfani da maƙabartar.
Maƙabartar da ta shafe fiye da shekaru 500 tana karɓar mamata da girmamawa, yanzu ta zama barazana ga rayuka da dukiyoyin mutane.
Yadda Maƙabartar Ta Samu Sunanta
An ce maƙabartar ta samo sunanta daga wata bishiyar kuka da ke tsakiyar ta, wadda aka ce Shehu Usman Ɗan Fodiyo ya taɓa ziyarta a lokacin da ya ziyarci Kano, inda ya yi wa mamata da ke ƙasa da bishiyar addu’a.
Daga Wurin Girmamawa Zuwa Maboya
A yau, wurin da ke da dimbin tarihi da daraja a zuciyar al’ummar Kano, ya zama inda ’yan daba ke boyewa da aikata laifuka kamar yanda Jaridar AMINIYA ta ruwaito
Wasu daga cikin laifukan da ake yawan samu sun haɗa da kwacen waya, sata, fashi da makami, da kuma satar ƙarafa da allunan kabari da ake sayarwa ga masu sana’ar ƙarfe.
Wani ma’aikacin maƙabartar da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, “Idan rana ta yi zafi ko kuma da dare, ’yan daba sukan fito suna aikata fashi. Har babur ɗin hawa an taɓa kwacewa.”
Masu Haƙar Kabari Na Cikin Halin Ƙunci
Shugaban masu haƙar kabari a maƙabartar, Malam Garba Sa’adu, ya ce ya shafe fiye da shekaru 40 yana aikin haƙa kabari a wurin, amma ba ya samun kulawa daga gwamnati.
“Ba wai kawai ana ba mu alawus kaɗan ba ne, hatta wata huɗu da suka wuce ba a biya mu ba. A wasu lokutan muna aiki cikin haɗari saboda babu tsaro ko da a cikin dare,” in ji shi.
Ya roƙi gwamnati da ƙungiyoyi masu zaman kansu da su tallafa wajen gyaran maƙabartar, cike ramukan kaburbura da kuma tabbatar da tsaro a yankin.
Martabar Maƙabartar Na Fuskantar Barazana
Malam Garba ya ce, “Wannan maƙabarta ba ta da tamka a tarihi. Amma idan aka bar ta a haka, za ta ci gaba da zama barazana ga al’umma. Ya kamata a yi wani abu kafin abin ya fi haka muni.”
Hukuma Ta Ce Za Ta Bincika
Mai magana da yawun Kwamitin Maƙabartu na Jihar Kano, Malam Aminu Yahaya Galadanci, ya ce kwamitin na da shirye-shiryen kai ziyara don duba halin da maƙabartar ke ciki da kuma ɗaukar matakan gyara.
“Ina kira ga jama’a da su riƙa sanar da mu irin waɗannan matsaloli kai tsaye domin mu ɗauki mataki cikin lokaci,” in ji shi.
Ina Gudunmawar Karamar Hukumar Dala?
Duk da cewa ƙaramar hukumar Dala ce ke da alhakin kula da maƙabartar, har yanzu ba a samu wani bayani daga shugabannin hukumar ba. Sai dai an ce akwai shirye-shiryen tattaunawa da bincike don magance matsalar.
