Connect with us

News

Ango Ya Yi Ajalin Amaryarsa Kwanaki Kaɗan Bayan Aure A Kano

Published

on

An tsinci wani lamari mai tayar da hankali a garin Gwarzo da ke Jihar Kano, inda wani ango ke zargin kashe amaryarsa da suka yi aure ba fiye da wata ɗaya ba.

Bayanai daga mazauna Sabuwar Unguwa, inda lamarin ya faru, sun bayyana cewa an jiyo ƙarar ihun matar kafin daga bisani aka kira jami’an tsaro domin kawo ɗauki. Sai dai kafin isowar su, matar ta riga ta sheƙa lahira sakamakon raunin da ta samu.

Advertisement

Kotu Ta Yi Watsi Da Ƙarar Akpabio Kan Dakatar Da Sanata Natasha

Rahotanni sun ce ango ya caccaki amaryar da wuƙa, lamarin da ya yi sanadin rasuwarta. Likitoci a asibitin da aka garzaya da ita sun tabbatar da mutuwarta.

Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta tabbatar da cafke wanda ake zargi, inda ta ce an fara gudanar da cikakken bincike domin gano musabbabin lamarin da kuma tabbatar da gaskiyar al’amari.

Advertisement

Hukumomi na ci gaba da gudanar da bincike yayin da al’umma ke ci gaba da bayyana alhini da mamaki kan wannan mummunan lamari da ya girgiza zukatan jama’a.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending