Connect with us

News

Bauchi: Gwamna Bala Na Shirin Ƙirƙirar Sabbin Masarautu 

Published

on

Gwamnatin Bauchi Ta Dakatar Da Ma’aikata 6 Kan Zargin Sayar Da Kadarorin Gwamnati

Gwamnatin jihar Bauchi ƙarƙashin jagorancin Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed ta buɗe ƙofar karɓar bukatun al’ummomi masu sha’awar kafa sabbin masarautu da kuma gundumomi a faɗin jihar.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai bai wa gwamnan shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Kwamared Mukhtar Gidado, ya fitar a ranar Litinin, inda ya bayyana cewa gwamnati na buɗe ƙofa ga masu neman a samar da sababbin masarautu ko kuma sabbin gundumomi da su mika ƙorafinsu cikin tsari.

Advertisement

Dan Majalisar Tarayya ya Maka Wasu Matasan Mazabarsa A Gaban Kotu A Kano 

Sanarwar ta bayyana cewa wannan mataki ya biyo bayan yadda gwamnati ke ƙoƙarin inganta tsarin mulki da tafiyar da al’amuran al’umma ta yadda kowane yanki zai samu wakilci da kuma ci gaban da ya dace da su.

A halin yanzu, jihar Bauchi na da masarautu guda shida – Bauchi, Katagum, Misau, Jama’are, Ningi da Dass. Sai dai a watan Disamba na shekarar 2024, gwamnatin Bala Mohammed ta amince da ƙirƙirar sabuwar masarauta ta Seyawa wadda za ta kasance da hedikwata a karamar hukumar Tafawa Balewa.

Advertisement

Gwamna Bala ya bayyana cewa kafa masarautar Seyawa na daga cikin kokarin gwamnatin sa na samar da zaman lafiya mai ɗorewa da kuma warware matsalolin da suka dabaibaye yankin tsawon shekaru sama da talatin.

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa karɓar takardun neman sabbin masarautu da gundumomi zai gudana daga ranar Talata 10 ga Yuni, zuwa Talata 8 ga Yuli, 2025. Takardun za a mika su ne a ofishin Babban Sakataren Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Harkokin Masarautu, Malam Abubakar Umar, da ke Sakatariyar Bauchi.

Advertisement

Gwamnatin jihar ta jaddada cewa za ta yi duba na musamman da bin ka’ida kan kowace bukata da aka mika, domin tabbatar da adalci da daidaito a cikin tsarin gudanarwar masarautu da gundumomi a jihar

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending