Connect with us

News

Da Tinubu Ba Shugaban Ƙasa ba Ne, Da Yanzu Yana Titi Yana Zanga-Zanga – Ndume

Published

on

Sanata Ali Ndume, ɗan majalisar dattawa mai wakiltar Borno ta Kudu, ya bayyana cewa da Bola Ahmed Tinubu ba shi ne shugaban ƙasa ba a yanzu, da kuwa yana kan titi yana jagorantar zanga-zanga kan yadda ake tafiyar da mulkin Najeriya.

Sanatan ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da tashar Arise Television, inda ya ce halin matsin tattalin arziki, hauhawar farashin kayayyaki da tabarbarewar tsaro da ake fama da su a fadin ƙasar nan, lamari ne da da can, Tinubu ba zai yi shiru ba a kai.

Advertisement

‎Gwamnan Kano Ya Ba Da Umarnin Gyaran Makarantar Koyon Faransanci Da Chinese 

“Idan wani ne ke mulki yanzu, da Tinubu yana kan titi yana zanga-zanga kamar yadda ya saba lokacin yana ‘dan gwagwarmaya,” cewar Ndume.

Sanata Ndume ya ce ko da yake mutane da dama suna ganin yana sukar gwamnati, shi kuwa bai damu ba, domin ba zai daina faɗin gaskiya kan yadda ake tafiyar da mulki ba.

Advertisement

Ya ce yana da yakini da irin rawar da yake takawa a majalisar dattawa, don haka ba zai yarda siyasa ta hana shi faɗin gaskiya ba.

“Ina jin kira daga wasu kusoshin gwamnati suna cewa in dawo cikin sahun masu goyon bayan shugaban kasa, amma ina fada musu cewa gaskiya ce a gabana. Ni ba na amincewa da duk wata manufa da za ta hana ni fadin gaskiya,” in ji shi.

Advertisement

Sanatan ya ƙara da cewa shi faɗaɗɗen ɗan gwagwarmaya ne, wanda ya saba tsayawa kan gaskiya, ko da kuwa hakan zai saka wasu su ƙyamar shi.

Tinubu Ya Saba Fitowa Kan Irin Wadannan Harkoki”

Advertisement

Ndume ya bayyana cewa irin salon mulkin da ake yi a yanzu, da can da Tinubu ne bai amince da shi ba.

“Idan a can ne ni ne shugaban ƙasa, ina aikata abubuwan da ake gani a yanzu, da Tinubu ya jagoranci zanga-zanga akan titi. Domin shi mutum ne da ke tsayawa akan abinda ya yi imani da shi,” in ji shi.

Advertisement

Ayyuka Da Nauyin Da Ke Kan Majalisar Dattawa

Sanata Ndume ya kuma bayyana cewa matsayin majalisar dattawa bai zama na amincewa da komai daga shugaban ƙasa kai-tsaye ba, illa idan ta ga cancanta.

Advertisement

“A tsarin dimokuraɗiyya, shugaban ƙasa shi ne ya kamata ya lallaba mu Sanatoci domin samun goyon bayan mu, ba wai mu ne za mu zama marasa ra’ayi ba. Shi ba shi da kuri’a a Majalisa, mu ne muke da kuri’a,” in ji shi.

Ya ce ko da yake yana da dangantaka da Tinubu a baya, hakan ba zai hana shi fadin gaskiya ba, domin ya san cewa Allah ne kaɗai zai iya ɗauke masa wannan matsayi.

Advertisement

Furucin Ndume ya tayar da mahawara a tsakanin ’yan Najeriya, inda wasu ke ganin yana faɗin gaskiya, wasu kuma na ganin yana kokarin shirya kansa ne don wata sabuwar manufa ta siyasa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending