Connect with us

News

YouTube Ta Sauya Ka’idojin Samun Kuɗin Talla

Published

on

images (1)

Dandalin YouTube mai mallakar kamfanin Google, ya sanar da sabon tsarin da zai shafi yadda masu ƙirƙirar bidiyo ke samun kuɗin talla, indaa ya bayyana cewa bidiyoyin da aka maimaita ko aka sarrafa da yawa ba za su ƙara samun kuɗin talla ba.

Sabbin ƙa’idojin, wadanda za su fara aiki nan ba da jimawa ba, sun sanya damuwa a zukatan masu ƙirƙirar abun ciki, musamman waɗanda ke amfani da fasahar kere-kere ta na’ura wato Artificial Intelligence (AI).

Advertisement

Hukumar Kula da Yansanda ta gurfanar da manyan jami’ai fiye da DUB 150 bisa zargin take hakkin fararen hula

Sai dai a cikin wani karin bayani da kamfanin ya fitar, YouTube ya bayyana cewa matakin ba ya nufin hana amfani da AI gaba ɗaya. “Muna maraba da amfani da kayan aikin AI wajen ƙarfafa bayani ko inganta labari. Kuma tashoshin da ke amfani da AI yadda ya kamata za su ci gaba da samun kuɗin talla,” in ji sanarwar.

Kamfanin ya ce burin wannan sabon tsari shi ne:

Advertisement

Tabbatar da ingancin abun da ake wallafawa,

Rage yawan bidiyoyin kwaikwayo ko marasa ƙima,

Advertisement

Da kuma kare haƙƙin masu ƙirƙira na asali

A cewar masana a fannin sadarwa da fasahar zamani, matakin na YouTube wani ƙoƙari ne na kare mutuncin dandalin da kuma tabbatar da cewa masu amfani da shi na samun sahihan bayanai da ingantattun bidiyo.

Advertisement

YouTube ta jaddada cewa masu ƙirƙirar da ke da ƙwarewa da gaskiya a cikin aikinsu, musamman waɗanda ke ƙirƙirar abun ciki na asali, za su fi amfana da wannan sabon tsari.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending