Connect with us

News

Ƙungiyar ASUU na shirin sake tsunduma yajin aiki

Published

on

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), ta yi gargaɗi cewa za ta iya sake tsunduma yajin aiki saboda gwamnati ta kasa cika alƙawuran da ta ɗauka.

Shugaban ƙungiyar, Christopher Piwuna, ya ce gwamnati ba ta kula da walwalar malamai, ba ta samar da kuɗaɗen gudanar da jami’o’i yadda ya kamata, kuma ba ta aiwatar da yarjejeniyar da suka cimma ba.

Makarantar Al’mumtaz Academy Keffi Za Ta Gudanar da Ranar Jawabi da ba da Kyaututtuka ta 2025- Inji Dr. Musa Ahmad Isa

Wannan na zuwa ne bayan Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ya bayyana cewa “Babu wata jami’a ko malaman ASUU da za su sake shiga yajin aiki” idan aka ci gaba da tattaunawa da kuma cika buƙatun malaman.

Sai dai ASUU ta ce hanyar da za a guji yajin aiki ita ce kawai a cika musu alƙawuran da aka riga aka amince da su.

Ƙungiyar ta bayyana cewa yawancin malamai suna koyarwa da gudanar da bincike ba tare da kayan aiki ko tallafi ba.

Wasu ma ba sa iya biyan kuɗin mota zuwa wajen aiki, biyan buƙatun yau da kullum, har ma da kuɗin makarantar ’ya’yansu.

Advertisement

 

 

 

AMINIYA

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending