News
INEC: Sama da Katin Zaɓe 360,000 Ba A Karɓa Ba A Kano
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa sama da katin zaɓe na dindindin (PVCs) guda 360,000 har yanzu suna hannunta ba tare da masu su sun zo karɓa ba a jihar Kano.
Kwamishinan Zaɓe mai kula da jihar Kano, Ambasada Abdu Zango, ne ya bayyana hakan a ranar Asabar, lokacin da yake karɓar tawagar Kwamitin Wayar da Kan Jama’a Kan Rijistar Kuri’a da gwamnatin jihar ta kafa ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya.
Ambasada Zango ya yi kira ga kwamitin da ya ƙara himma wajen wayar da kan jama’a kan muhimmancin karɓar PVC da kuma yin rijistar zaɓe. Ya ce kafa wannan kwamiti wani mataki ne da zai taimaka wajen samun nasara a shirin rijistar masu zaɓe.
“Ina da kwarin gwiwa kan cewa wannan kwamiti zai taka muhimmiyar rawa wajen ganin an cimma nasarar shirin, ganin irin ƙwarewar mutanen da aka zaɓa cikin kwamitin da kuma shugabancin Kwamared Waiya,” in ji shi.
Ya tabbatar wa kwamitin cewa hukumar INEC za ta ba su cikakken goyon baya domin ganin an cimma nasu manufofi.
A nasa jawabin, shugaban kwamitin kuma Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya ce sun kai ziyarar ne domin sanar da hukumar manufar kwamitin da kuma ayukan da za su gudanar, bisa umarnin Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Kwamared Waiya ya bayyana cewa kwamitin ya ƙunshi wakilai daga sassa daban-daban na al’umma, ciki har da jam’iyyun adawa, tare da manufar ƙarfafa ‘yan ƙasa su fito su yi rijistar zaɓe da kuma karɓar PVC.
Ya kuma yi kira ga INEC da ta ƙara rumfunan zaɓe a jihar Kano domin rage cunkoso a ranakun zaɓe. Haka zalika, ya bukaci hukumar da ta bayar da goyon baya wajen sauƙaƙe ayyukan kwamitin.
Kwamared Waiya ya sake jaddada kudirin gwamnatin jihar Kano na samar da yanayi mai kyau don ganin an sami nasarar shirin rijistar zaɓe a jihar.
