Connect with us

News

Jihar Borno Ce Ta Fi Kowace Jaha Yawan Masu Rajistar Katin Zaɓe Ta Yanar Gizo – INEC

Published

on

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa sama da ƴan Najeriya miliyan 6.2 ne suka kammala rajistar katin zaɓe ta yanar gizo a matakin farko na shirin ci gaba da rajistar masu zaɓe (CVR) da ake gudanarwa a faɗin ƙasar.

A sabon rahoton mako na shida da hukumar ta fitar a ranar Litinin, an bayyana cewa mutum 6,232,673 ne suka kammala rajistarsu tsakanin 22 zuwa 28 ga Satumba, 2025.

Advertisement

INEC ta ce mata sun fi maza yawa cikin masu rajistar da mutum 3,250,338 (kashi 52.15%), yayin da maza suka kai 2,982,335 (kashi 47.85%).

Matasa masu shekaru 18 zuwa 34 ne suka fi rinjaye da adadin 4,230,715, yayin da dalibai suka kai 1,565,824. Haka kuma, mutane masu bukata ta musamman sun kai 137,865.

Advertisement

Rahoton ya nuna cewa Jihar Borno ce ta fi kowace jaha yawan masu rajista da adadin 682,805, inda ta doke Osun da ta samu 599,363, da kuma Legas da 555,442.

Sauran jihohi da suka biyo baya sun haɗa da ,Kebbi – 472,662, Ogun – 450,897, Kaduna – 376,054, Kogi – 298,194, Kano – 290,690, Yobe – 258,693, Abuja (FCT) – 227,397

Advertisement

A ƙasan jerin kuma, Enugu ta samu mafi ƙarancin adadi da mutum 5,092, sai Abia da 5,225, Ebonyi da 6,935, da Edo da 10,278.

INEC ta ƙara da cewa a mako na biyar (22 – 26 ga Satumba), mutane 1,004,132 ne suka kammala cikakken rajista – ciki har da 537,743 da suka yi ta yanar gizo da 466,389 da suka yi ta ofis.

Advertisement

 

 

Advertisement

PUNCH

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending