News
An Kama Wani Da Ake Zargi Da Kashe Matarsa Da Gatari Bayan Bikin Haihuwar Ɗansu
Rundunar ‘yan sandan jihar Edo ta kama wani mutum da ake zargi da kashe matarsa da gatarinsa a bayan gida, bayan gudanar da bikin zagayowar ranar haihuwar ɗansu mai shekara biyu a Auchi, karamar hukumar Etsako West ta jihar.
Wani mazaunin yankin ya shaida wa manema labarai cewa wanda ake zargin, da aka bayyana da suna TJ, ya kashe matarsa mai suna Queen ne a ranar Talata, 30 ga Satumba, bayan sun kammala bikin tare da danginsu.
Yadda Wani Manomi Ya Rasa ‘Ya’yansa Biyar A Hatsarin Jirgin Ruwa
“Ba mu ji wata hayaniya ko rikici tsakaninsu ba a daren ranar. Mun kwanta barci kamar yadda aka saba. Amma da safe ba su fito ba. Sai ɗansu ƙarami ya fito da jini a jikinsa, amma ba shi da rauni. Da muka shiga ɗakin ne muka tarar da Queen kwance cikin jini, wuyanta a sare,” in ji wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa.
Bayan aikata laifin, TJ ya tsere daga wurin kafin isowar jami’an tsaro, abin da ya sa rundunar ‘yan sanda ta fara bincike tare da ƙaddamar da farautarsa.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Edo, CSP Moses Yamu, ya tabbatar da cewa an kama wanda ake zargin a ranar Lahadi a Benin City, babban birnin jihar.
