News
Bamu Da Cikakkun Kayan Aikin Yaƙi Da Ƴan Ta’adda —Babban Hafsan Soji Najeriya
Babban Hafsan sojin Najeriya Laftanal Janar Olufemi Oluyede ya ce jami’an tsaron ƙasar ba su da wadatattun kayan aiki da zai kai su ga yin nasara a yaƙi da ƴan ta’adda.
Sabon Babban Hafsan Sojin na wannan batu a lokacin da yake jawabi a gaban zauren majalisar dattawan Najeriya, a wani ɓangare na tantanceshi, domin tabbatar da naɗin da shugaban ƙasar Bola Tinubu ya yi masa.
An Damfari Wata Mata Euro 3,300 Bayan Da Aka Sayar Mata Da Kokwanba A Matsayin Tsabar Zinari
Laftanal Janar Olufemi ya ce kowa ya san cewa babu wadatattun kayan aiki, a don haka abu ne mai matuƙar wahala a iya yaƙi da ƴanta’adda da ƴanbindiga da sauran ɓatagari a faɗin ƙasar.
Oluyede ya yi kira ga gwamnatin tarayyar Najeriya da ta ƙarfafa ayyukan ƴansanda a sassan ƙasar.
Tuni Majalisar Dattawan ƙasar ta amince da naɗin Laftanal Janar Olufemi a matsayin Babban Hafsan Sojin Najeriyar.
A makon da ya gabata ne shugaba Bola Tinubu ya sanar da sauke manyan shugabannin tsaron ƙasar, a dai-dai lokacin da ake raɗe-raɗin cewa wasu sojoji sun fara yunƙurin juyin mulki, wanda gwamnatin Najeriyar ta musanta.
