News
Shugaba Tinubu Na Duba Yiwuwar Naɗa Janar Christopher Musa A Matsayin Sabon Ministan Tsaro
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na duba yiwuwar naɗa tshohon Shugaban Hafsoshin Tsaro na ƙasa, Janar Christopher Musa, domin ya maye gurbin Mohammed Badaru Abubakar a kujerar Ministan Tsaro, bayan da Badaru ya yi murabus saboda dalilan akan lafiyar sa.
Majiyoyi daga fadar shugaban ƙasa sun ce ana ci gaba da nazarin takardun Janar Musan, wanda ya shahara wajen jagorantar yaƙi da ƙungiyoyin ta’addanci a Arewa maso Gabas da wasu sassan ƙasar nan.
Rahotannin cikin gida sun nuna cewa gwamnati na kallon Janar Musa a matsayin wanda zai iya ɗaukar nauyin kujerar, musamman ganin yadda matsalolin tsaro ke ƙara ta’azzara a wasu yankuna.
A yanzu haka ba a fitar da sanarwar hukumanci ba, sai dai ana sa ran shugaban ƙasa zai bayyana matakin na ƙarshe a makonni masu zuwa.
