Connect with us

News

‎Aƙalla Mutane 9,854 Ne Ke Ɗauke Da Cutar AIDS A Yobe 

Published

on

FB IMG 1764716719221
Spread the love

‎Gwamnatin Yobe ta bayyana cewa aƙalla mutane 9,854 ne ke ɗauke da cutar AIDS a jihar, kuma dukkaninsu na karɓar maganin ceton rai.

‎Hukumar ta tabbatar da cewa waɗannan marasa lafiya suna rayuwa cikin ƙoshin lafiya, tare da rage yiwuwar yaɗa cutar ga wasu.

MAAUN’s Rapid Rise Shakes Up Nigeria’s Private University Rankings

‎Babban Daraktan Hukumar Kula da Cutar AIDS ta Jihar Yobe (YOSACA), Dakta Jibril Adamu Damazai, ne ya bayyana cewa Yobe na da mafi ƙarancin adadin masu ɗauke da cutar a ƙasar nan da kashi 0.4%, inda ya danganta hakan da dabarun yaƙi da cutar da ake aiwatarwa a jihar.

‎“Ba mu tsaya a kan wannan nasara ba, muna ƙara ƙoƙari don rage yawan kamuwa da cutar,” in ji shi.

Advertisement

‎Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ta kashe sama da Naira miliyan 120 wajen sayen kayan gwaji, abin da ya bai wa ƙungiyoyi damar gano mutanen da ba a san suna ɗauke da cutar ba a cikin al’umma, domin a ba su magani.

‎A cewarsa, Yobe na kan gaba wajen daidaita dabarun yaƙi da cutar AIDS, musamman ganin yadda ake samun sauye-sauye a kuɗaɗen da ake kashewa a duniya.

‎Dakta Damazai ya kuma bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta fara shirye-shiryen samar da magungunan ƙwayar cutar HIV a cikin gida.

‎Ya yaba da jajircewar gwamna Mai Mala Buni, wanda ya ƙara kuɗaɗen da ake bai wa hukumar kula da cutar AIDS da kashi 400%, tare da samar da katafaren ofis na dindindin ga hukumar.

Advertisement

 

AMINIYA

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *