News
An Kama Matashi Bisa Yunƙurin Shigar Da Tabar Wiwi Gidan Gyaran Hali A Kano
Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Ƙasa (NCoS) reshen Jihar Kano ta ce ta kama wani matashi mai shekaru 20 bisa zargin yunƙurin shigar da tabar wiwi ga wasu ɗaurarru ta hanyar ɓoye ta a cikin burodi.
A wata sanarwa da kakakin hukumar, CSC Musbahu Lawan K/Nassarawa, ya fitar a ranar Alhamis, ya bayyana cewa an kama matashin mai suna Muhammad Kabir, dan unguwar Hotoro Tishama, ne a harabar Babbar Kotun Jihar Kano.
Dakarun Sojin Sama Sun Hallaka Sama Da ‘Yan ISWAP 10 A Yankin Timbuktu Triangle
Sanarwar ta ce jami’an hukumar da ke bakin aiki a gidan gyaran hali na Gwauron Dutse sun gano tabar wiwin da aka kunshe a cikin burodi yayin da matashin ke yunƙurin baiwa wasu ɗaurarru da aka kawo kotu domin sauraron shari’arsu.
“Mun cafke wanda ake zargin ne bayan jami’anmu sun gano haramtattun kayan da ya ɓoye a cikin burodi, da nufin miƙa wa ɗaurarru,” in ji sanarwar.
Kakakin ya ƙara da cewa Kwantarola na NCoS a Kano, Ado Inuwa, ya bayar da umarnin miƙa matashin ga Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) domin ci gaba da bincike tare da ɗaukar matakan doka da suka dace.
Hukumar ta jaddada cewa za ta ci gaba da tsaurara matakan tsaro a cibiyoyin gyaran hali domin hana shigar da duk wani abu da zai iya kawo cikas ga tsarin gyara da tarbiyyar ɗaurarru.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
